1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe mutane a Coci

Abdul-raheem Hassan
June 5, 2022

Akalla mutane 50 sun mutu wasu da dama sun jikkata a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kan wata majami'ar Katolika da ke jihar Ondo, yayin da suke Ibada a karshen mako.

https://p.dw.com/p/4CJ9w
Nigeria Demo gegen Polizeigewalt in Lagos
Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture-alliance

Hukumomin tsaro a Najeriya ba su yi karin bayani kan gano maharan da kuma dalilin kai harin ba, sai dai a wata sanarwa da ya fitar bayan katse ziyararsa a Abuja abyan harin, gwamnan jihar Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu ya ce za a cigaba da farautar maharan, tare da mikasu gaban kotun don hukunci.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa hari ne mai ban tsoro. Irin wannan farmaki kan mabiya dai ba sabon abu bane a Najeriya, sai dai a baya-bayan nan an fi yawaita ayyukan ta'addanci satar mutane ne a wasu yankunan arewacin kasar.