Sabuwar dokar zabe a Najeriya ta tilasta amfani da nau’ra
October 24, 2018Bayan daukar dogon lokaci da kuma kin sanya hannu akan dokar da shugaba Muhammadu Buuhari ya yi. Majalisar dattijai ta yi wa sabuwar dokar gyara inda ta tilasta amfani da naurar domin tabbatar da ingantaccen zabe.
Sau uku ana kai wa shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari dokar zaben yana kin sanya hannu a kanta bisa abinda ya kira saba ka’ida a sauye-sauyen. A yanzu dai majalisar tace ta gyara dukkan sassan da ya haifar da takaddama ta kuma amince da dokar a karo na hudu.
Sassa masu muhimmanci da aka gyara a dokar sun hada da amfani da nau’rar tantance katin zabe wato “Card Reader” da Najeriyar ta fara amfani da ita a zaben 2015, a yanzu dokar ta halasta yin haka da ma cewa idan babu wannan kati to babu zabe.
A sabuwar dokar zaben ‘yan majalisar sun kayyade kudin takardar takara ta neman shugaban kasa a kan Naira miliyan goma, na gwamna Naira miliyan biyar, sannan dokar ta kayyade kudadden da aka amince dan takara ya kashe a kan Naira biliya biyar ga shugaban kasa, na gwamnan kuma kada ya wuce Naira biliyan daya, na sanata kuma Naira miliyan 250 dan majalisar tarayya kuma Naira miliyan 100. Duk wata gudamawa da za’a ba dan takara kar ta wuce Naira miliyan goma.
Dadewar da aka yi ana jan kafa a kan wannan doka wadda a baya majalisar ta gaza kaiwa ga yi mata gyaran fuska ya sanya jefa tababar cewa an makara idan har za’a iya amfani da ita a zaben da ya rage kwanaki 114.
Abin jira a gani a wannan karon shi ne ko shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari zai sanya hannu a dokar zaben da ke da muhimmancin gaske.