1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Najeriya: Majalisa ta bukaci da a rage kudaden aikin hajji

Uwais Abubakar Idris
April 26, 2024

Kwamitin kula da aikin hajji a majalisar wakilan Najeriya ya nanata cewa wajibi ne a rage kudin aikin hajjin bana saboda darajar da takaradar kudin Najeriya ta Naira Naira ta yi.

https://p.dw.com/p/4fEJf
Hoto: Amr Nabil/AP Photo/picture alliance

Wannan zai samar da sauki ga maniyatan Najeriyada a bana suka biya kudi mafi tsada a tarihin aikin hajjin kasar. Wannan na faruwa dai dai lokacin cikar wa'adi  na sabon tsarin da aka bullo da shi.

Kwamitin kula da aikin hajjin na majalisar wakilan Najeriya da ya kamala gudanar da wani taron sia kan lamarin, ya bayyana cewa korafe-korafen da yake ci gaba da samu daga alummar Najeriyar ne ya tilasta mashi gudanar da taron sirri a kan lamarin domin tunkrar hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya.

Saudi-Arabien, Mekka | BG Haddsch
Hoto: APAimages/IMAGO

Domin kama daga batun bukatara rage kudin aikin hajjibisa ga farashin dalla da babban bankin kasar ke sayarwa da ma batun  kudin guzuri da aka rage da na masaukai a kasar Saudiyya duka sun duba su tare da bukatar daukan mataki.

Yanayi na hawa da saukan kudin dalla a Najeriya ya haifara da babban kalunale a game da batun aikin hajjin na wannan shekarar, wannan ya sanya maniya biyan kudin aikin hajji mafi tsada a kasar da ya sanya a wannan shekarar. 

Saudi-Arabien, Mekka | BG Haddsch
Hoto: Sajjad Hussain/AFP/Getty Images

A wannan shekarar dai hukumar kula da aikin hajji ta Najeriyar ta bayyana cewa kasdar Saudiyya ta bullo da sabon tsari na tsara alhazai rukuni rukuni na mutane 40, kuma a wannan juma'ar ce wa'adin na  wannan tsari ke cika. Ko ina aka kwana a game da maniyatan Najeriyar?

Majalisar wakilan Najeriyar dai ta bayyana aniyarta ta yingyara kan dokar da ta samar da hukumar kula da aikin hajji ta Najeriyar. A wannan shekarar dai mahajatta sama da dubu 50 ne ake sa ran zasu samu aikin  hajji daga Najeriyar sabanin sama da dubu 90 da aka saba inda wasu kasashen