Kwaskwarima a hukumar EFCC a Najeriya
June 3, 2019Majalisar dokokin Najeriyar ta yi gyaran fuskar kan dokar da ta kafa ga hukumar ta EFFC ne tare kuma da shafe wasu sassa takwas da ke zaman ginshikin kafa hukumar da aka kafa tun a shekarar 2004. Masu sharhi na kallon wannan matakin da cewa zai iya karya lagon hukumar wacce ke da karfin bankado duk wadanda suka tara kudaden haram da maciya amanar kasa. Tuni kungiyoyin fararen hula masu yaki da cin hanci da rashawa a Najeriyar da na lauyoyin kasar suka yi kira ga shugaban Najeriya Muhamadu Buhari da ya guji sanya hannu kan dokar domin matakin ya sabawa bukataun 'yan Najeriya da ma alwashin gwamnatin kasar na yaki da cin hanci da rashawa. Sai dai gwamnatin Najeriyar ta ce dole ne ta sanya majalisar yin nazari kan dokar, saboda karfin ikon da take da shi na yin gyara kan ababen da duk taga sun cancanci a kawo masu gyara, ko da yake hurumin amfani da dokar a yanzu ya rage ga amincewar da shugaban Najeriyar zai yi kan dokar da idan har ya rattaba mata hannu za a iya soma aiki da ita. A baya dai shugaban ya sha kin sanya hannu a wasu dokokin da majalisar ta amince da su hannu bisa cewa sun sabawa manufofin ci-gaban kasa.