1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kara farashin man fetur a Najeriya

July 2, 2020

Hukumar Kayyade Farashin Man Fetur da Dangoginsa a Najeriya PPPRA, ta kara farashin man fetur a kasar, inda a yanzu za a rinka sayar da shi kan kudi Naira 140 da kwabo 80 zuwa Naira 143 da kwabo 80.

https://p.dw.com/p/3eiY2
Nigeria Tankstelle in Lagos
KArin farashin man fetur a Najeriya, ya janyo mayar da martaniHoto: AFP/Getty Images/P. U. Ekpei

A watan Maris din wannan shekarar ne dai gwamnatin Najeriyar ta sanar da rage farashin man fetur din zuwa Naira 123, sai dai kuma kwatsam a Larabar wannan makon Hukumar Kayyade Farashin Man Fetur da Dangoginsa ta kasar PPPRA, ta sanar da cewa za a rinka sayar da man fetur din kan kudi sama da Naira 140.

A Alhamis din wannan makon kuma dokar fara sayar da man vetur din kan kudi Naira 140 da kwabo 80 zuwa Naira 143 da kwabo 80, ta fara aiki a fadin kasar baki daya. Tuni dai masana da masu fafutuka suka fara sukan wannan lamari da suke ganin talaka zai dandana kudarsa, ganin cewa da ma al'umma na cikin matsin tattalin arziki, baya ga ta'azzara la'amura da annobar cutar coronavirus da ta addabi duniya ta yi. 

Su ma dai al'ummar kasar sun fara mayar da martani kan batun na karin farashin man fetur din, ganin yadda suke fama da radadin matsin tattalin arziki. Mutane da dama dai suan rasa ayyukansu a kasar, sakamakon matakan hana zirga-zirga da gwamnati ta dauka da nufin dakile yaduwar annobar cutar coronavirus da ta addabi duniya.