Najeriya: Martani kan nemo 'yan matan Chibok
April 14, 2017An dai share shekaru har guda uku ana faman nema amma kuma an share shekaru ukun ba labari a cikin karatun 'yan mata 'yan makaranta na Chibok da kungiyar Boko ta haramun tai nasarar sacewa can baya. A daukacin wannan mako dai batun na 'yan matan ne ya dauki hankali ciki dama wajen kasar. To sai dai kuma an kare cikin takkadama a tsakanin gwamnatin Tarayya da ke fadin tayi rawar gani da kuma 'yan kungiyar da ke fadin an kasa.
Karfin kungiyar Boko Haram ya rage sosai
Duk da cewar dai Abujar ta yi nasarar kassara karfin kungiyar ta Boko ta haramun dai, gaza gano 'yan matan dai na zaman tabo mai girma ga gwamnatin ta masu neman sauyi da tazo a bisa alkawarin kai karshen yakin, dama kila gano 'yan matan na Chibok. Bikin da ya kalli jerin tattaki da addu'o'i sannan da lacca, daga baya na zaman sake tuni ga gwamnatin da ke da jan aikin gano ragowar yan matan 195 da ke a hannun 'yan kungiyar. Abun kuma da Abujar ke fadin ta shirya tsaf da nufin kaiwa ya zuwa yin duk wadda ke yi domin gano 'yan matan a fada ta shugaban kasar da ya aike sako na musamman ga iyayen 'yan matan.
Kokarin gano sauran 'yan matan Chibok
Koma ya zuwa yaushe ne dai ake iya kaiwa ga tabbatar da tattaunawar gano ragowar 'yan matan dai, gwamnatin ta yi nisa a cikin tunkahon ceto 24 na 'yan matan da suka bi ruwa a karkashi na tsohuwar gwamnatin 'yan lema. Abun kuma a tunanin Mallam Nasiru El Rufai da ke zaman gwamnan jihar Kaduna kuma jigo a cikin jam'iyyar APC mai mulki ya sanya karkatar da laifi ya zuwa inda ya dace. Abun jira a gani dai na zaman yanda take iya kayawa a tsakanin 'yan fafutukar da gwamnatin kasar a bisa hanyar kai karshen takkadamar 'yan matan da ke zaman wasu a cikin dubbai na mutanen da suka bi shannun sarki a cikin rikicin na shekaru kusan Takwas da Najeriya ke fama da shi.