PDP ta yi watsi da sakamakon zabubbuka
March 12, 2019Jam'iyyar PDP da ta mayar da murtani a kan zabubbukan gwamnonin da na ‘yan majalisar dokoki na jihohi da lafazi mai zafi bisa abinda ya faru a wadanan jihohi guda shida, tana cewa ba zai yiwu ba a ce duka jihohin da ta kama hanyar samun nasara aka fuskanci matsala ta bukatar sake zaben.
Ta ce ba zata lamunci matakin hukumar zaben ba a kan hukuncin da ta yanke a zabubbukan gwamnonin a jihohin Kano, Plateau, Bauchi Sokoto, Benue da ma Rivers, tana zargin akwai makarkashiya ta yunkurin murdiya daga hukumar zabe da ma gwamnatin da ke mulki a jihohi wadada na jamiyyar APC ne. Mr Kola Ologbondiyan na mai bayyana cewa.
Ya ce: "Hukumar zabe ta zama ‘yar siyasa don ta mika 'yancin da take da shi yadda ta tsayar da sanar da sakamakon zaben ba tare da wani bayyani ba a jihohin da PDP ta kama hanyar samun nasara. Don haka ba zamu yarda da duk wani yunkuri na magudi ba, zamu tabbatar da cewa mutanenu sun kare kuru'un da aka baiwa jamiyyarmu da ‘yan takararmu".
Ganin cewa jam'iyyar APC da hukumar zabe ne aka nunawa ‘yar yatsa a wannan sarkaniya ta zabubbukan gwamnonin na jihohin Najeriyar musamman wuraren da ake kankankan tsakanin PDP da APC. Ko me jam'iyyar APC zata ce a kan wannan zargi na yunkurin murde zaben ganin jihohin da aka ayyana za'a sake zabe a wasu yankunansu su na da yawa? Ibrahim Kabir Masari shi ne sakataren walwalar jama'a na jamiyyar APC:
Tuni dai hukumar zaben ta bayyana cewa akwai tsari na doka ga batun zabe a Najeriya. Ko me zasu ce a game da zargin hada baki don yiwa wata jamiyya makarkashiya? Malam Aliyu Bello shi ne jam'in yada labaru ne na hukumar zaben Najeriyar.
A yanzu dai kalo ya koma a kan hukumar zaben da zata sake zabubbuka a wasu mazabu a jihohin musamman inda babu wata tazara mai yawa a tsakanin jamyyun biyu. Kamanta adalci a zaben zai kara nuna matsayin da dimakurdiyyar Najeriyar take shekaru ashirin bayan sake kafa tsarin a kasar.