1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta sake shiga matsalar karayar tattalin arziki

November 23, 2020

Jim kadan da sake shiga masassarar tattalin arzikin a Najeriya, muhawara ta barke cikin kasar tsakanin masu adawa da hukumomin kasar.

https://p.dw.com/p/3lj6I
Erdölindustrie in Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/G. Esiri

Kasa da 'yan awoyi da sake shiga masassara ta tattali na arzikin Tarrayar Majeriya, muhawara ta barke cikin kasar tsakanin masu adawa da ke zargin gwamnati da kunne na kashi da hukumomin Najeriyar da ke fadin an yi rawar gani a halin Covid-19.

Duk da cewar dai sabuwar masasarar na zaman batu na tattalin arzikin kasar tuni ta rikide ya zuwa ga siyasa inda jiga-jigai na masu adawar Tarrayar Najeriyar suke fadin rashi na karbar shawara na zaman uwa ubar fadawar kasar cikin yanayin maras kyau.

Kama daga jam'iyyar PDP ta adawa ya zuwa ga Atiku Abubakar da ya yi mata takara a zaben da ya shude dai, tunani ya zo iri guda kan yiwuwar kaucewa matsalar, da 'yan mulkin sun bi shawarar al'ummar kasar.

Rashin sani na hanyar tsira dai a fadar Sanata Umaru tsauri da ke zaman sakataren jami'iyyar PDP ta adawa shi ya kai kasar ya baro ta a cikin tsakiyar rudani.

Karancin na gwamna masu gida rana a hannun jama'a
Karancin na gwamna masu gida rana a hannun jama'aHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Sai dai tuni mahukuntan kasar suka ce masassarar na zaman gajeruwar da kila za ta kare ya zuwa karshen wannan shekara.

An dai ruwaito ministar kudin kasar Zainab Ahmed na fadin kasar ta yi rawar gani cikin tsarin da ya kalli rushewar da ta kai har kusan kaso 50 cikin 100 a wasu kasashe na nahiyar Afirka.

Faduwar farashin man fetur da raguwa ta bukatarsa ce dai ake ta'allakawa da faduwa ta tattali na arzikin kasar da ke dogaro da bakar hajjar.

Najeriyar dai ta kalli masassarar da babu irinta shekaru sama da 30 baya. Kuma a fadar Barrister Isma'il Ahmed da ke zaman kakakin jam'iyyar APC, "masu adawa na kasar ba su da bakin magana a cikin rikici na tattali na arzikin Tarrayar Najeriyar a halin yanzu."

Sabon rahoton hukumar kididdiga ta kasar dai ya ce a zango na uku na shekarar bana tattalin arzikin Najeriya ya tsuke da kusan kaso 3.6 cikin 100 duk da hobbasar da kasar ta gani a cikin harkokin sadarwa da na noma.

Kuma a fadar Malam Lawal Habeeb da ke zaman wani masani a harkar ta tattalin arzikin kasar "wasu manufofin 'yan mulkin da suka hada da kari na farashin man fetur da kudin wuta na da ruwa da tsaki da sabuwar masassarar da ke ta ta da hankali."

Tuni dai hukumomi na jihohi da ita kanta tarraya suka fara nuna alamun gajiyawa ga batun sauke nauyin albashi da ma bukatu na 'yan kasar cikin tsarin da ya kalli tsukewar kudin shiga da karuwa ta bukatu na tallafin al'umma.