Matsalar man fetur ya addabi 'yan Najeriya
January 4, 2018Talla
Duk da cewa yanzu kamfanin man kasar na NNPC ya yi nasarar kai karshen matsalar a Legas da ke zama cibiya ta kasuwanci da Abuja babban birnin kasar ga dukkan alamu har yanzu da sauran aiki game da makomar harkar man fetur da al'ummar kasar ke dogaro a kai. Tashin farashin gangar danyen man ta sanya ba riba a tunanin manyan dillalan man da ke cewar suna tafka asara mai yawa wajen shigo da man daga waje sannan su sayar a kan farashin Naira 145 kan kowace lita.