1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

MTN ta yi gargadin katse layuka a Najeriya

Ramatu Garba Baba MAB
June 15, 2021

Matsalar tsaro a kusan duk sassan Najeriya ta soma haifar da tsaiko inda katafaren Kamfanin MTN ya yi barazanar dakatar da ayyukansa a kasar mai dimbin al'umma.

https://p.dw.com/p/3uyW8
Afrika | Mobile money
Hoto: imago/UIG

Kamfanin sadarwa na MTN a Najeriya, ya ce matsalar tsaro ta soma shafar hanyoyin sadarwa, saboda haka ne ta yi barazanar dakatar da ayyukanta nan bada jimawa ba. A wata sanarwa da fitaccen kamfanin ya fitar, ya ce, yana cike da takaici a tsaikon da jama'a masu amfani da hanyar sadarwar za su iya fuskanta a sakamakon rashin zaman lafiya da ake fama da shi a sassan kasar.

Kamafanin mallakin kasar Afrika ta Kudu, na da rassa a kasashen duniya kimanin ashirin, amma Najeriya ta kasance babbar kasuwarta, inda miliyoyi daga cikin al'ummar kasar suka raja'a ga kamfanin na MTN.

Kasar mai al'umma fiye da miliyan dari biyu, ta sami kanta cikin matsaloli da suka hada da rikicin kabilanci da na masu son ballewa daga kasar, da kuma 'yan bindiga da masu sace mutane suna neman kudin fansa. Matsalolin da ke ci gaba da shafar tattalin arzikin kasar.