Kokarin sasantawa da ASUU a Najeriya
June 23, 2022Gwamnatin Najeriyar dai ta sanya al'ummar kasar zuma a baka, musamman iyaye bayan da ta ce an kusa kawo karshen yajin aikin. Jami'an gwamnatin kasar dai na ci gaba da tattaunawa a kokarin kawo karshen yajin aikin da mallaman jami'o'' mallakarta suka shiga tun ranar 14 ga watan Fabarairun wannan shekarar, abin da ya gurgunta daukacin tsarin karatun jami'o'i a Najeriyar. Ministan kwadago da ingantuwar aiki na Najeriyar Dakta Chris Ngige ne ke jagorantar tawagar gwamnati a tataunawar, inda bayanai suka nuna cewa an kusa kammala dukkanin batutuwa da suka shafi albashi da ma alawus-alawsu na malaman jami'o'in.
A hannu guda kuma gwamnatin na fatan hadawa da batun ma'aikatan jami'o'i wadanda ba malamai ba da suma suke yajin aikin, domin kar a yi kitso da kwarkwata. Koda yake ana fatan kai wa ga cimma matsaya dangane da yajin aikin, sai dai har yanzu akwai batu na manhajar biyan albashi da malaman jami'o'in suka nuna damuwarsu a kai wato IPIS da ake amfani da ita abin da ya sa suka tsara tasu manhajar. Yajin aikin da malaman jami'o'in suka tsunduma dai ya zama dan kullum a Najeriya, abin da ke shafar tasiri na ilimi a makarantu. Ana jira a ji sakammakon wannan tattaunawa da bangarorin biyu ke yi a asirce, ko za ta zama dalilin farantawa iyayen yara rai da tun 14 ga watan Fabarairun bana suke zaune a gida a yanayi na rashin tabbas.