Najeriya: Soke layukan salula marasa shaida
December 16, 2020Sabuwar dabarar dai na zaman kokari na mayar da martani ga karuwar ayyukan 'yan ina da kisa da masu karbar fansa da ke ta kara yaduwa a Najeriya. Wayoyin na salula dai na zaman daya a cikin manyan kayan aiki na masu aikata ta'asar. Kuma a cikin tsawon makwanni biyun da ke tafe ko dai duk wani dan kasar da ke bukatar amfana daga layin na salula ya kai ga tabbatar da samun lambar ta dan kasa da ke iya tantance shi da daukacin al'ummar Najeriyar sama da dari biyu ko kuma ya koma ga tsoffafi na dabarun aiken sako.
Hanyar gano masu aikata laifin yin garkuwa da mutane ko yin ta'addanci
Najeriyar dai ta dauki lokaci tana kallon karuwar na laifukan da wayar ta salula ke iya kaiwa ga tsarewa a cikin tsari na zamani ta yanar ta gizo. To sai dai kuma gaza yin nisa a cikin samun lambar na iya zama matsala ga kasar da ke da layukan salula sama da miliyan 180. Dr Abubakar Sadiq Hussaini dai na zaman kwararre a harkar ta salula, a jami'ar Amirka da ke garin Yola a Najeriyar, da kuma ya ce sabon tsarin na iya taimaka wa Najeriya a neman hanyar rage radadin rashin tsaron.
Ko gwamnatin za ta iya a wannan hanya da ta kama da nufin rage matsalar rashin tsaron
Majiyoyi a ma'aikatar sadarwar Najeriyar sun ce ana cigaba da ka ce na ce a tsakanin manyan kamfanoni na salula na kasar da ke kallon shirin a matsayin kokarin rage musu kudade na shiga, da kuma gwamnatin kasar da ke fadin tsaro na zaman na kan gaba da batun kudin shiga. Wani abin da ke iya shafar yunkurin dai na zaman karancin na yawa masu rijistar shaidar ta 'yan kasa da a cewar kabir Adamu da ke zaman masani a harkar ta tsaro ke iya shafar nasarar shirin tsakanin al'umma.