Najeriya na fushi kan wulakanta 'ya'yanta a Kamaru
July 13, 2017A cikin farkon wannan mako ne wani rikicin biyan harajin kwale-kwale ya yi sanadiyar kisa na 'yan Najeriya kusan 100 a yankin Bakassi da Jamhuriyar kamaru ke iko a kansa a yanzu. Ana zargin jami'an tsaron Kamarun da kai hari a kan mazaunan na Bakasi da ake zargi da kin biyan harajin a wani abun da ke zaman na baya-baya nan cikin takkadama tsakanin al'ummar yankin.
Harin ya harzuka mahukuntan tarrayar Najeriyar da ke masa kallon karya yarjejeniyar unguwar Green Tree ta kasar Amirka da ta tanaji zama a cikin 'yanci a bangaren al'ummar tarrayar Najeriyar da ke yankin da kotun duniya ta mika wa Kamaru.
Tuni fadar mulki ta Abuja ta mika sammaci ga jakadan kamaru da ke tarrayar Najeriyar, sannan kuma tana shirin tura ministocinta biyu zuwa Yaoundé da nufin nunin bacin ranta, a cewar ministan cikin gidan tarrayar Najeriyar Abdurahman Bello Dambazau.
Sai dai bacin ran tarrayar najeriyar bai tsaya a kan cin zarafin 'ya'yanta da ke a Bakassin ba, tuni ma dai ya tsallaka zuwa ga 'yan gudun hijirar Boko Haram da kamarun ke tilasta wa dawowa gida cikin halin kunci. Abun da Abujar ke kallon ba daidai ne ba, sannan kuma ya saba wa ka'idar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.
Akalla 'yan Najeriya 2,600 ne kamarun ta tilasta wa dawowa cikin gida. Ko a karshen wata Yuni an tasa keyar wasu 'yan gudun hijirar 887 ya zuwa garin Banki da ke kan iyaka ta kasashen guda biyu. Abin kuma da har ila yau ministan cikin gidan tarrayar Najeriyar ke kallon cewa an saba .
Ana kallon kasancewar Paul Biya a Abuja da kuma ziyara shugaba Muhammadu Buhari zuwa birnin Yaoundé sun taka muhimmiyar rawa wajen sauyin yakin da a baya ya nemi gagarar kundila tsakanin kasashen biyu. Da tsoma bakin manyan kasashen duniya irin nasu Amirka da Faransa ne aka kai ga sulhunta tsakanin makwabtan kasashen Najeriya da kamaru.