Najeriya na gudanar da zaben cike gurbi a jihohi 26
February 2, 2024Kama daga 'yan majalisar dattawa da wakilai da masu takama da yin doka a jihohi, akalla mazabu 35 a jihohi 26 ne ke fuskantar sabobbin zabuka a tarrayar Najeriya a ranar Asabar (03.02.2024). Wannan ne karon farkon fari da hukumar INEC ke sake fuskantar 'yan zabe tun bayan babban zaben cikin Najeriyana shekarar 2023. Hajiya Zainab Aminu da ke zaman kakakin hukumar zabe ta ce shiri ya kamalla a sassan kasar a banagren INEC da ake masa kallon damar wankin suna da kila ma kima bayan rikici mai zafi na siyasa a cikin Najeriya.
Karin bayani: Rahoton masu sa ido a zaben Najeriya ya bar baya da kura
Akwai tsoron kauracewar zaben a bangaren miliyoyi na 'yan kasar da ke ji a jiki sakamakon matsin tattalin arzikin da ke zaman ruwan dare gama duniya a Najeriya a halin yanzu. Amma sabon zaben na zaman zakaran gwajin dafi ga sabuwar gwamnatin kasar ta Najeriya da ke da jan aikin wajen tabbatar da 'yancin zabe a tsakanin al'umma ta kasar. Shehu Musa Gabam da ke zaman shugaban jam'iyyar SDP na kasa ya ce sun yin shirin taka rawa a zabukan komai rintsi.
Karin bayani: Najeriya: Sake tsara bayanan na'urar BVAS
Jami‘an 'yan sanda sun bayyana takaita zirga-zirga daga safiyar Jumma'a zuwa ranar Asabar da za a gudanar da zabe a daukacin jihohin 26 da abin ya shafa. Sai dai tun kafin a kai ga ko'ina, aka fara ganin alamun rudu a cikin shirin hukumar zaben INECa jihohin kasar da daman gaske. A jihar Plateau ga misali, takardun zaben da suka isa birnin Jos ba sa dauke da alamar lemar jam'iyyar PDP, abin da ya tayar da hankalin masu lemar da ke fadin cewar ana ta kokarin danne masu dama, a cewar Timothy Golu, jigon PDP a jihar.
‚