EFCC: Ceto tattalin arzikin Najeriya
April 24, 2024Hukumar Yaki da Almundahana da Kudin Al'umma da yi wa Tattalin Arziki Zagon Kasan EFCC dai, ta ce ta gano wasu kafofin internet da dama da ke ci gaba da cin karensu ba babbaka a fanin hada-hadar kudi ne ke ci gaba da zamewa hadari ga tattalin arzikin kasar da ma takardar kudinta wato Naira. Ta ce bayan kafar hada-hadar kudi ta Crypto da Binance, akwai dandali na kafafen sada da dama da suma ke yin hada-hadar kudin wanda kuma hakan ke dada rusa darajar kudin kasar wato Naira.
An dai gano kiyasin wata hada-hada irin wannan da ta kai ta kimanin dalar Amurka biliyan 15 a mu'amala da dandali daya kawai cikin shekara guda rak, abinda EFCC din ta ce ya tilasta mata rufe dandali kimanin 300 kawo yanzu domin samar da maslaha a kasuwar hada-hadar kudin kasar. Darajar Naira dai ta sake yin kasa a kasuwar hada-hadar kudin kasar bayan da ta daga da kaso 50 cikin 100 a kwanakin baya-bayan nan, kafin kuma kwatsam a wayi gari ta sake yin kasa idan aka kwatanta da dalar Amurka ko da ya ke babban bankin kasar na CBN ya sanar da sake antaya miliyoyin dalolin Amurka cikin kasuwar hada-hadar kudin da nufin ceto Nairar.