Najeriya: Neman mafita daga matsalar tattalin arziki
August 4, 2016Sun dai dauki lokaci suna kai kawo, sun kuma gwada dabaru dabam-dabam. To sai dai daga dukkan alamu karatun yana neman wucewa da sanin gwamnatin Tarrayar Najeriya da yanzu haka ta koma ga kwarraru da nufin samo hanyar warware matsalar da tattalin arzikin kasar ke fuskanta.
Najeriya dai ta yi nisa a cikin yanayin masassarar tattalin arzikin da ta kamata kuma ke kara tasiri a cikin lamura na kasar.
Kasa da kaso 20 cikin 100 na yawan kudin shigar da kasar ke tsammani ne dai yanzu haka ke kaiwa ga jihohi da ma ita kanta tarrayar kasar da ta kalli farfasa bututun man fetur sannan kuma da faduwar darajarsa a kasuwanni na kasa da kasa.
Jin ra'ayin kwararru na tattalin arziki
To sai dai kuma gwamnatin da a baya ta kai ga bullo da jerin matakai da nufin shawo kan lamuran amma ba nasara, yanzu haka ta koma ga jin ra'ayin kwarraru a harka ta tattalin arzikin kasar da nufin fitar da a'i cikin sarkakiyar da take fuskanta a halin yanzu.
Ya zuwa yanzu wasu manyan masana a harkar ta tattalin arziki guda hudu ne dai gwamnatin ta gaiyyata da nufin nazarin tsare-tsaren tattalin arzikin kasar na shekaru biyun da ke tafe a cewar ministan kasafin kudin kasar Udoma Udo Udoma.
"Mun gana da wasu masanan tattalin arziki da suka hada da Bismack Rewane da Farfesa Abanikoro da Dr Ayo Teribo da Farfesa Badayi Sani da Dr Bode Agusto, sun mana bayanai ga kwamitin tattalin arzikinmu domin sanin martanin su ga matsakaicin shirin tsarin tattalin arzikinmu, kamar yadda kaidar harkokin kudinmu ta tanada. Wannan na zaman wani bangare na tattaunawa mai fadi da masu ruwa da tsaki da harkokin tattalin arzikinmu domin sanin yadda za mu fita a cikin masassarar da tattalin arzikinmu ke ciki a yanzu."
Abujar dai na da fatan jerin tattaunawar da a makon da ya gabata ya kaita ga ganawa da kungiyoyi na farar hula sannan kuma a makon gobe za ta kunshi 'yan kasuwar kasar na iya kaiwa ga ceto kasar daga barazana ta durkushewar aljihu.
Talauci da fatara a birni da kauye
Ya zuwa yanzu dai kudin kasar na Naira na kara kasa sannan kuma fatara na dada ratsa kauyuka da birane a cikin tsarin da daga dukkan alamu kasuwa ke neman kasa zama alkali mai adalci.
To sai dai in har tarrayar ta dau 'yar tattaunawa da nufin neman mafita, wasu a cikin jihohin kasar ma sun yanke shawarar mika wani bangaren ikonsu ga jama'ar gari cikin gwajin sa'ar da kasar ke fuskanta yanzu.
Abubakar Sani Bello shi ne gwamnan jihar Neja da ke arewacin kasar, jihar kuma da tuni ta mika aikin tace ma'aikata da ma biyan albashi ga kungiyar kwadago da nufin kauce wa rikicin kudin da jihar ke ciki a halin yanzu.
"'Yan kwadago da kansu suka ce za su tace mana wadanda yake su ne ainihin ma'aikata domin gano ma'aikatan bogi da ke karbar albashi ba bisa ka'aida ba. Kudaden albashin da muke biya ya zarta yawan wanda kungiyar kwadagon ta nuna mana bayan bincike da kuma lissafin da ta yi. Na ji dadin wannan abin. Su din ma za mu ba wa kudin su rika biya suna kuma tace ma'aikata na hakika. In an samu nasara to su taimaki jihar Neja baki daya."
Tarrayar Najeriyar dai na fatan samun karin kudin shiga na haraji da ma kila kyawun kakar noma na iya kaiwa ga rage radadin da ya kai har a tsakar ka a yanzu.