Najeriya: NLC ta ce yajin aiki ba gudu ba ja da baya.
September 26, 2018Kungiyar kodago ta kasa a Najeriya ta ce babu gudu babu ja da baya a yunkurinta na tafiya yajin aikin sai baba ta gani. Yayinda gwamnatin kasar ke cewa tana iyaka bakin kokarinta bangaren ‘yan kodagon na cewa wasan yara ne kuma kokari ne na yaudarar ma‘aikatan. Wani tarton manema labarai na hadin gwiwa a tsakanin manyan kungiyoyin kodagon kasar guda Uku ya kare tare da daukacin ma’aikatan kasar yanke hukuncin tsunduma cikin yajin aikin na sai baba ta gani .
Ma’aikatan sun ce suna shirin kulle tashoshin jiragen sama da cibiyoyin hakar man fetur dama daukacin kafafofin tara kudade na gwamnati da nufin aikewa da sako ga gwamnatin da suke zargi da kokarin yaudarar ma’aikata.
Duk da cewar an tsara wani taron manyan jami’ai na kungiyoyin guda Uku na NLC da TUC da ULC da ministan kodagon kasar da nufin lallashi sannan da shirin tsomin baki a bangaren shugaban kasar in hali ya kama, daga dukkan alamu kasar na shirin ganin baki a bangaren masu kodagon dake fadin tura ta kai bango kuma hakuri ya kare musu.
Comrade Kabir Nasir na zaman kakaki na kungiyar ULC da kuma yace sun shirya tsaf kuma sun yi nisa ga duk wani kokari na sauya tunanin yan aikin tun daga tsakar daren wannan rana ta Laraba. Karya da yaudara cikin halin rudu ko kuma kokari na murde wuyan mahukunta dai, tuni dai abujar ta tsara jeri na matakai da nufin hana yajin aikin dake zaman irin san a farko kuma ke iya tasiri ga gwamnatin dake komawa zabe .
Ko bayan wani taro a tsakanin manyan jami’ai na kodagon da ministan kodagon kasar chris Ngige, an kuma tsara yiwuwar mataimakin shugaban kasar zai saka baki duk dai da nufin ganin kasar bata tsunduma yajin aikin ba.Tarrayar Najeriyar dake biyan Naira dubu 18,000 a matsayin mafi karancin albashi dai na zaman daya a cikin koma baya ga batun albashin a daukaci na kasashen yammacin Africa.