Rikita-rikitar siyasa a Najeriya
August 12, 2021A daidai lokacin da babban zaben Tarayyar Najeriyar ya rage kasa da shekaru biyu, rikicin siyasa musamman ma na cikin gida na kara kamari. Tun da fari dai an yi ta samun 'ya'yan babbar jam'iyyar adawar kasar PDP na sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki ta APC, cikinsu har da na baya-bayan nan wato gwamnan jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yammacin kasar mai fama da rikicin 'yan binidga masu garkuwa da mutane.
Ko a farkon wannan wata na Agusta da muke ciki ma dai, sai da wasu manyan jiga-jigai a babbar jam'iyyar adawar ta PDP mai alamar lema suka yi murabus, a abin da suka bayyana da rashin gamsuwa da tsarin gudanar da jam'iyyar da bangaren shugabanninta.
Sai dai ba wai babbar jam'iyyar adawar ta PDP ce kawai ke fama da rikicin cikin gidan ba, domin kuwa haka abin yake ga APC jam'iyyar da ke shan romon mulki tun daga shekara ta 2015 kawo yanzu. An yi ta samun tashin-tashina gabanin babban taron jam'iyyar na kasa da nufin zaben sababbin shugabanni, biyo bayan rikicin da ya taso kan hallacin kwamitin riko na jamiyyar a karkashin gwamnan jihar Yobe wanda wasu 'yayan jam'iyyar ta APC ke bayyana haramcin shugabancin rikon a karkashin dokokin tsarin mulkin kasar, abin da kuma ke haifar da takaddama a tsakaninsu.