Najeriya: Rikicin 'yan takarar shugaban kasa a PDP
April 25, 2022Kawance tsakanin ‘yan takarar neman kujerar shugabancin kasar Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP ya rushe ne bayan samun matsaloli na rashin fahimta a tsakaninsu.
Hon Aminu Waziri Tambuwal na cikin ayarin ‘yan tafiyar da ke neman a tasayar da shi takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP.
‘’Maimakon a ce an tsayar da mutum guda, an ce an tsayar da mutum biyu, wannan me ya nuna maka? akwai wata magana a ciki. A tambayi Malam Muhammadu Hayatudden, a tambayi Sanata Bukola Saraki, a tambayi kauran Bauchi gwamnan jihar Bauchi shin tsakaninmu da Allah mun yi wannan zaman muka ce wannan abun ba zai yiwu ba ko bamu yi wannan zaman ba, muka ce mun dakatar da wannan abu?’’.
To menene na dawowa a ce an tafi Minna bayan mu da muka sa kanmu muka gayyato mai girma shugaban kasa Babangida shi kuma shi ya gayyato wadannan dattawan muka ce mu da muka sa kanmu mun tsayar da wannan abun, to bayan mun tsaida shi akwai wanda ke da hurumin ya dawo ya ce dole ya dawo da mu ya sa sai mun karbi abun da ya ke so ya yi?.
To amma sai dai gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad daya daga cikin masu neman takarar ya yi na’am da matakin kungiyar dattawan Arewa, kuma ya ce sam bai da wata masaniya kafin daukar wannan mataki na zabar su.
‘’Babu wanda zai sa shi tilas, kuma ya riga ya kafa kwamitin yakin neman zabensa yana yi, saboda haka abun da ya yi mu mun yi alkawari ba za mu je muna rigima da shi ba, matukar ya kare mutuncinsa ya kare mutuncinmu. Wannan abun ba abu ne na fada ba, an riga an wuce nan, ya ce zai ci gaba da neman fafatawa mu ma zamu fafata amma da goyon bayan dattawan arewa da sauran mutanen arewa, ba zamu yi sake ba zamu fita tukuru mu nema’’.
Yanzu haka ma dai daruruwan magoya bayan gwamna Tambuwal na ta bayyana mubaya’a ga matakin da gwamnan ya dauka na jan daga don a fafata. Hon Abdullahi Yusuf Hausawa wani mai goyon bayan gwamna Tambuwal ne.
‘’Kowa ya na da dama ya yi takara, kuma kowa ya na da dama ya je ya yawata cikin kasa ya nemi magoya baya. Kuma wannan matsayar da mai girma gwamna ya yi, mu a matsayinmu magoya bayansa kuma ‘yan jihar Sokoto mun gamsu da ita kuma mun yarda da ita, mun yi imani da cewa Allah shi ke bayarwa’’.
Farfesa Yahaya Tanko Baba shugaban sashen koyar da kimiyyar siyasa a jami’ar Usmanu Danfodiyo ya yi tsokaci kan abun da suke ganin ya haifar da wannan zabe da kungiyar Dattawan Arewan ta yi.
’Yankuna da wadannan ‘yan takar suka fito a cikin arewa, shi Bkola Saraki ya fito daga yankin arewa ta tsakiya, shi kuma Kauran Bauchi ya fito daga yankin arewa maso gabas, sannan gwamnan jihar Sokoto ya fito daga yankin arewa maso yamma ya na iya zama wani abu da wadannan dattawa suka yi la’akari da shi’’.
To amma kuma tuni ‘yan jam’iyyar APC mai mulki a Najeriyar ke ta bayyana yadda wannan rikicin na jamiyyar PDP zai zama garabasa a garesu.
‘’Dama ce garemu mu samu jajirtaccen dan takara daga yankin kudu domin ya samu wannan mulkin, mu mara masa baya a ci gaba da aiwatar da ayukkan alkhairi a tarayyar Najeriya ga ‘yan Najeriya’’.
Tuni dai wasu daga cikin masu nuna sha’awa ga takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP ke bayyana cewa matakin na kungiyar dattawan Arewa ACF ra’ayi ne kawai, ba matsayin jam’iyyar PDP ba.