1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan sabon kasafi

Abdullahi Tanko Bala
July 10, 2020

A kokarin tunkarar matsalar tattalin arziki na tarrayar Najeriya da annobar corona ta kassara, shugaban kasar Muhammad Buhari ya rattaba hannu kan sabon kasafin kudin da kasar ke fatan zai taimaka wajen rage radadi.

https://p.dw.com/p/3f7dt
Nigeria Abuja | Prsident Muhammadu Buhari ernennt Ibrahim Gambari zum Stabschef
Hoto: Reuters/Nigeria Presidency

Kasafin na Trilliyan 10.8 na zaman sabon fata a cikin tarrayar Najeriyar na sake tashi tsaye bayan faduwar tattalin arzikin kasar sakamakon covid19.

Tuni shugabannin gwamnatin ta Abuja suka ce suna shirin farawa da gudu a cikin neman hanyar kaiwa ga cimma nassarori da dama ga kasar  dake cikin yanayi mara kyau yanzu. Shugaban kasar yace zuwa karshen watan Yuli daukacin hukumomin gwamnatin kasar za su samu akalla kaso 50 cikin dari na kudade na manyan aiyyukan dake cikin kasafin domin tabbatar da tasirin da ‘yan kasar ke shirin gani.

Nigeria National Assembly
Shugaba Buhari a zauren majalisar dokokiHoto: Nigeria Office of the House of Representatives

“Dukannin ministoci za su habbaka kokarin aiwatar da manyan aiyyuka sannan kuma su hada kai da ma'aikatar kudi da tsare-tsare domin samun nasarar kasafin. Mun kuma samu cigaba a kokarin aiwatar da tsohon kasafin kudin kasar . Ya zuwa watan Mayun da ya shude mun saki abun da ya kai  Naira Biliyan 253.3 domin manyan aiyyuka. Kuma ma'aikatar kudi da tsare-tsaren kasafi na shirin sakin kudade na manyan aiyyuka domin ganin kowace ma'aikata ta samu abun da bai gaza kaso 50 na kudaden manyan aiyyukanta ba.”

Sabon kasafin dai ya fifita agaji a sassa daban daban na rayuwar yau da gobe ko bayan manyan ayyuka da gwamnatin ke fatan iya kaiwa ga sauya rayuwa tsakanin kowa cikin kasar a fadar Sanata Ahmed lawal dake zaman shugaban majalisar dattawa da kuma ya jagoranci tabbatar da sabon kasafin.

Nigeria Kabinett Muhammadu Buhari Präsident
Shugaba Buhari da 'yan majalisar ministocinsaHoto: Reuters/A.Sotunde

Duk da cewar dai ana sa ran rage radadi da kamar wuya kasafin ya kai ga share hawayen kowa ko kuma daukar kasar ta Najeriyar daga masassarar da ta kai kusan kaso hudu a cikin dari na tattalin arzikin.

To sai dai kuma a fadar Hon Umar El Yakub mai baiwa shugaban kasar shawara a harkokin majalisa ya fitta zakka a kokarin fitar da A'i cikin sarkakiya da duhu.

An dora  sabon kasafin ne bisa dalar Amurka 28 kan kowace  ganga, a yayin kuma da za'a canji kowace dalar Naira 381. A wannan mako ne dai Abujar tace ta fara shirin kasafin na badi da ta tsara zai isa zauren majalisun kasar ya zuwa watan Satumba duk da nufin murkushe matsin tattalin arzikin dake zaman barazana mai girma ga kasar.