Rabuwar kawuna a Najeriya na kara yawaita
May 26, 2023An kira bambancin kabila an kuma ambato sashen kudancin kasar da Arewa da ma masu neman a raba ko bayan uwa uba batun addini, duk a kokarin samar da shugabancin kasar da ke zaman mai tasiri. Kuma bullar Bola Ahmed Tinubu da zabin mai taimaka masa dai, ta farraka kai har a tsakanin 'yan bokon da ke da al'adar mantawa da batun bambanci wajen kisa da shan romo na ganima a cikin kuryar daki. Masana na kasar dai na kallon rabuwar na zaman wadda babu irinta, tun bayan yakin basasar kasar shekaru 53 da suka gabata. Kuma jan aikin da ke gaban sabon shugaban dai, na zaman kokarin lallashi ko kuma murde wuya cikin neman sake mai da kowa hanya a kasar da ke da babban rikici. Kasar kuma da a cewar Shehu Gabam da ke zaman shugaban jam'iyyar SDP na kasa, na fuskantar barazanar rugujewa daga ko-in-kula na gwamnatin da ke shirin barin gado.
In har tana nuna alamun lalacewa cikin kasar da ke da fatan sauyi, rage kaifi na rashin adalcin ne ke iya kai wa zuwa ga mantawa da bana, a fadar Reverand John Hayab da ke zaman shugaban kungiyar addinin Kirista ta kasar CAN reshen jihar Kaduna, kungiyar kuma da a baya ta nuna bacin rai da irin tsari na shugabanci na siyasa ta kasar. Kungiyoyin addinai da kabilu iri-iri a Tarayyar Najeirya dai, ba su boye adawa da takara da kila ma bullar Tinubun a shugabancin kasar ba. Kuma a cikin al'ada, kungiyoyin ne ke zaman na kan gaba a adawa da kila kokarin farraka ga gwamnatin. Faruk BB Faruk dai na sharhi cikin batun na siyasa da kuma ya ce iya tunkarar batun tattalin arziki a bangaren sabon shugaban kasar, na iya kai wa ya zuwa dinke da dama cikin kasar a nan gaba. 'Yan kwanakin da ke tafe dai na da tasirin gaske ga takun rawa ta sabuwar gwamnatin APC, a kokarin sauya abubuwa da dama a cikin Tarayyar Najeriyar.