1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Yadda kabilanci ke shafar siyasar Najeriya

May 31, 2022

Wasu 'yan siyasa a sassan kudu da tsakiyar Najeriya na sukar matakin tsayar da Atiku Abubakar da PDP ta yi a matsayin wanda zai yi mata takara a zaben 2023.

https://p.dw.com/p/4C68h
Vor Wahlen in Nigeria Atiku Abubakar
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Alamba

Yan kwanaki da kai wa da bullar Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban tarrayar Najeriya kuma a yanzu a matsayin dan takara na jam'iyyar PDP a zaben na shugaban kasar Najeriya a badi, siyasa ta kabilanci na neman sake kunno kai a cikin Najeriya da ke kara nuna alamun rabuwa a tsakanin sashen arewacin kasar da kudancinta.

Nigeria Rotimi Amaechi
Amaechi ya yi zargin nuna kabilanci a zaben fid da gwaniHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi

Kama daga shi kansa tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi da ya ce, an hada kai an masa kabilanci wajen zaben fidda gwanin mai tasiri, ya zuwa dattawan kudancin kasar da ke fadin ba su shirya zaben na Atiku Abubakar bisa hujjar sabawa alkawari dai, sannu a hankali zuciyar mai tsumma na kara baki a sassa dabam-dabam cikin kasar a halin yanzu.

Duk da cewa, har ya zuwa yanzun jam'iyyar APC mai mulkin Najeriyar ba ta kai ga fitar da dan takara na zaben na badi ba. Tuni dama PDP tai tanadi na kujerar tare da tura mukami na shugaban jam'iyyaar da ma shi kansa shugaban kwamiti na amintattu zuwa sashen arewacin kasar a cikin neman tabbatar da kujerar a kudu, kafin Atiku da ke zaman ta ba zato ba kuma tsammani. Nasarar kuma da ko bayan dagun hakarkari ke neman mai da kasar cikin tsananin rikicin sashen arewacin kasar da kudancinta.

Arfika Nigeria APC Abuja
Jam'iyyar APC na fama da rikicin cikin gidaHoto: Ubale Musa/DW

To sai dai ko bayan jam'iyyar PDP ita kanta APC da ke shirin zaben fidda gwanin, na fuskantar rikicin da ke dada kamari a cikin jam'iyyar. Duk da cewa,  wani taron shugaban kasar da gwamnonin jam'iyyar ya kare da ranar wannan Talata a Abuja ba tare da kai wa ya zuwa ga yanke hukuncin in da masu tsintsiyar ke shirin fuskanta ba.

Rinjaye a kokari na tabbatar da ma su takara, ko kuma kokarin raba kai cikin kasar, kare taron APC a cikin makon nan dai na shirin nuna makoma ta kasar a cikin rabuwar da ke kara nuna alamun kamari yanzu. Fitar da dan takarar APC a arewa dai na nufin babakere na masu takarar yankin a zaben na badi, abun kuma da ke iya janyo karin dagun hakarkari cikin kasar a nan gaaba.

Makonnin da ke tafe, na da tasirin gaske ga makoma ta kasar da ke a tsakanin dorawa zuwa gaba dama rabuwar kai har a tsakanin manyan 'yan boko na tarayyar Najeriya a gabanin babban zaben na 2023.