Najeriya: Sake duba afuwar Niger Delta
May 26, 2016Ministan kasa a ma'aikatar albarkatun man fetir a Najeriya Emmanuel Ibe Kachikwu ya bayyana a ranar Alhamis din nan cewa akwai bukatar gwamnati ta samar da sauyi kan shirin yin afuwa ga mayakan sa-kai a yankin Niger Delta dan duba zargin da suke na nuna musu halin ko'inkula daga bangaren gwamnati da ma kamfanoni na kasa da kasa da ke aikin hakar albarkatun mai a yankin.
Jawabin ministan na zuwa ne bayan kai farmaki kan wasu kaddarori na aikin mai mallakar kamfanin Chevron a yammacin ranar Laraba da 'yan tawayen na Niger Delta Avengers suka ce su ne suka kai shi, abin da kuma ke zuwa a dai dai lokacin da dattawa a yankin ke cewa shigar dakarun sojan Najeriya a yankin ba zai kai ga warware wannan matsala ba.
A cewar ministan duk jihohin yankin kamata ya yi su ba da wakilai hudu zuwa biyar da za su rika aiki da jami'an tsaro dan ba da kariya ga kaddarorin kamfanonin da ke aikin hakar mai a yankin.