1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Najeriya ta ce za a hukunta Saraki

Uwais Abubakar Idris/ LMJOctober 30, 2015

Wata kotu a Najeriya ta yi watsi da bukatar da shugaban majalisar dattawan kasar Bukola Saraki ya gabatar dangane da tuhumar da kotun da'ar ma'aikata ke yi masa.

https://p.dw.com/p/1GxC4
Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki
Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola SarakiHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja fadar gwamnatin Tarayyar Najeriyar ce ta yi watsi da bukatar ta Saraki na kalubalantar hallacin kotun da'ar ma'aikata ta saurari shari'ar zargin kin bayyana kadarorinsa da ya mallaka da ake masa. Kotun ta ce dole ne Saraki ya fuskanci shari'a a kotun da'ar ma'aikata wacce ta kebe ranar biyar ga watan Nuwamba mai zuwa domin ci gaba da shari'ar. Daya daga cikin alkalai uku da suka yi shari'ar ya nuna adawa da wannan hukunci, sai dai bai yi wani tasiri ga sakamakon shari'ar ba. Barrister Mahmud Abubakar Magaji shi ne lauyan da ke kare Sanata Bukola Saraki ya kuma shaidawa waklilinmu na Abuja Uwais Abubakar Idris cewa za su dauki matakin daukaka kara kan wannan hukunci zuwa kotun koli.