1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sauya tunanin tsofaffin 'yan Boko Haram

Al-Amin Sulaiman MuhammadAugust 2, 2016

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar shirin nan na sauya tunani da kuma gyara dabi'u na tsofafin 'yan Boko Haram da suka ajiye makamai tare da mika kansu ga gwamnati.

https://p.dw.com/p/1JaUn
Boko Haram Kämpfer
Hoto: picture alliance/AP Photo

Gwamnatin tarayyar Najeriya ce ta kirkiro da wannan shiri na sake tunanin da rage tsatsauran ra'ayi na mayakan Boko Haram da suka ajiye makamansu tare da mika wuya ga gwamnatin don yi musu afuwa tare da mai da su cikin al'umma. An yi imanin cewa dole sai an rungumi wannan hanya kafin kawo karshe wannan yaki da tsari na kasa da kasa suka amince da shi bisa dokoki na Majalisar Dinkin Duniya.

Ana kallon wannan mataki a matsayin wata hanya ta samar da zaman lafiya mai dorewa bayan samun nasarar kaiwa ga karshen yaki da Boko Haram da ke ganin an cimma gagarumar nasara zuwa yanzu. J

anar Ashafa shi ne shugaban wannan shiri, ya shaidawa DW cewa ''gwamnatin tarayyar Najeriya ta tsara wannan shiri ne kamar yadda aka masa lakabi a turance domin bude kafa ga daruruwan mayakan Boko Haram da suka tuba suka mika makaman su domin yi musu afuwa da gyara musu dabi'u da horar da su sana'o'i domin dogaro da kai da kuma sake shigar da su cikin al'umma''.

Ana sa ran fara horar da wadannan matasan kowane lokaci daga yanzu wanda hukumomin ba su fayyace yawon lokacin da za'a dauka a horar da wadan nan matasa ba da ake kiyasin yawansu ya kai 800. Akwai hukumomin gwamnatin tarayyar Najeriya goma sha hudu da kuma kungiyoyin ba agaji da kungiyoyin fararen hula da shugabannin addinai da za su gudanar ayyukan sake dabi'un matasan da cire musu tsatsauran ra'ayi a zukatansu.

Nigeria Abuja Präsident Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari na son ganin an sauya tunanin tsofaffin 'yan Boko Haram don su zama mutane na gariHoto: picture-alliance/dpa/W. Krumm

Gwamnatocin jihohin shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya sun ce za su baiwa shirin dukkanin goyon baya da ya kamata kamar yadda gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya bayyana inda ya ke cewa ''za mu baiwa shirin dukkanin goyon bayan da ya kamata tunda dole sai an yi wannan tsari domin dawo da wadannan bayin Allah cikin al'umma don wanzar da zaman lafiya''.

Yayin da al'umma ke bayyana fargaba kan wannan shiri da ma yiwuwar komawar wadan bayin Allah cikin sauran al'umma da suka yaka a baya, rundunar sojoji da sauran hukumomin gwamnatin sun nemi jama'a su kwantar da hankulansu don kuwa matasan za su zama 'yan kasa na gari masu kyawawan dabi'u na zama da jama'a.