1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauyin sheka a siyasar Najeriya

Nasir Salisu Zango MNA
January 27, 2020

Guguwar sauyin sheka a tsakanin 'yan siyasar Najeriya na ci gaba da kawo cikas ga ci-gaban dimokuradiyya da tabbatar da akidar siyasa a kasar.

https://p.dw.com/p/3Ws7n
Nigeria - Wahlkampf
Hoto: Getty Images/AFP/L. Tato

Yanzu haka dai ya zama wata al'adar 'yan siyasar Najeriya yin hijira su sauya sheka zuwa wata jam'iyyar da Da Da zarar sun ga wacce suke ciki ta rasa mulki lamarin da ke kara kawo tsaiko ga dimokuradiyya.

Matsalar tattara komatsai da sauyin sheka a tsakanin 'yan siyasar Najeriya na ci gaba da zama ruwan dare gama duniya a tsakanin manya da kanann 'yan siyasa, akidar da a baya take zama sunnar siyasa yanzu ta zagwanye galiban 'yan siyasa, sun fi mayar da hankali kan abin da zai zo aljihunsu, don haka zamansu a jam'iyya ya ta allaka da irin maikon da suke lasa.

A makon jiya dai shugaban jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Kano, Injiniya Rabiu Suleman Bichi ya tattara kayansa ya koma jam'iyya mai mulki ta APC, jim kadan bayan da kotun koli ta tabbatar da korar karar da jam'iyyar da Rabiu Suleman Bichin ke jagoranta.

Yaya makomar kwankwasiyya bayan sauyin shekar shugaban jam'iyyar PDP a jihar Kano?
Yaya makomar kwankwasiyya bayan sauyin shekar shugaban jam'iyyar PDP a jihar Kano?Hoto: DW/T. Mösch

Ko da yake ba wannan ne farau ba da 'yan siyasa ke yin kaura daga jam'iyya zuwa jam'iyya ba, sai dai wannan ya zama wani abin gwajin lissafi har ta kai masana a harkokin siyasar Najeriya cewar siyasa "ta shiga uku a kasar".

Dr Maude Rabiu Gwadabe, tsohon malami ne a jami'ar Bayero ta Kano kuma shugaban jaridar Kanofocus ya ce wannan sauyin sheka ba fa wani sabon lamari ba ne shi ma na Kanon da ake ganinsa bawai dalili ne ya kawo domin "sauya sheka dabi'a ce ta 'yan siyasar Najeriya".

To ko mene ne makomar kwankwasiyya da jam'iyyar PDP a jihar Kano a wannan kaka ta sauyin sheka? Abubakar Ibrahim ya fadi ra'ayinsa yana mai cewa ai dama 'yan siyasar Najeriya da manya da kanana ba su da tabbas, kuma yanayin da aka shiga yanzu alamu ne na "rugujewar wata jam'iyya".

To amma ga matasa masu imani da kwankwasiyya takensu shi ne ba su fara don su daina ba, don haka sun ce duk da guguwar ficewar wadannan jiga-jigai na can baya irinsu Aminu Dabo da kuma Rabiu Suleman Bichi da ya bi sahu, su kam sun ce suna nan a cikin wannan tafiya ta kwankwasiyya.