1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari: Al'umma su yi zabe ba fargaba

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 22, 2019

A karo na biyu cikin wata guda, al'ummar Najeriya na shirin tunkarar rumfunan zabe a ranar Asabar domin kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki.

https://p.dw.com/p/3Dpup
Nigeria Prof. Mahmoud Yakubu (L) Präsident Muhhamadu Buhari
Shugaban hukumar zaben Najeriya INEC Farfesa Mahmoud Yakubu da shugaban kasa Muhhamadu BuhariHoto: Imago/Zuma

Hakan dai na zuwa ne mako guda bayan da humura zaben kasar INEC ta dage babban zaben kasar sa'o'i kalilan gabanin kada kuri'a a ranar 16 ga wannan wata na Fabarairu da muke ciki, tare da bayyana ranar 23 ga watan na Fabarairu a matasayin ranar da za a gudanar da zaben. Hukumar ta INEC dai ta ce hakan ya zama tilas bayan wasu matsaloli da suka sha kanta. Tuni ma dai shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari da ke neman wa'adi na biyu, ya gudanar da wani jawabi ga al'ummar kasar a jajiberin zaben, yana mai tabbatar musu da cewa su fito su kada kuri'unsu ba tare da fargaba ba, kasancewar an shirya tsab domin tabbatar da tsaro, abin da ke nuni da cewa zaben ka iya gudana a ranar Asabar din kamar yadda a ka tsara.