Najeriya: Sufurin jiragen ruwa da ke kyautata muhallin Lagos
Birnin kasuwanci na Lagos a Najeriya wanda ruwa ya kewaye ya yunkuro don amfani da sufurin jirgin ruwa wajen rage cunkosa a tituna tare da inganta muhalli.
Taikata lokaci ga fasinjoji a tafiyar jirgin ruwa
Tafiyar da a baya ake yin ta cikin sa'o'i uku zuwa wajen aiki yanzu ta koma gajera ta hanyar amfani da jirgin ruwa a cikin teku. Lagos, mai kimanin mutane miliyan 16 shi ne birnin mafi girma a Najeriya. Tuni wannan tafiya daga unguwanin talakawa zuwa Lagos Island, inda galibin ofisoshi suke, ta koma ana yin ta cikin mintuna 30.
Layin sayen tikiti
Tashar jirgin ruwa ta Ikorodu na ganin fasinjoji a kowacce safiya. A yayin da galibin mutanen Lagos ke zaune a unguwanni nesa da teku, galibin ofisoshi na a unguwar Victoria Island, Ikoyi da Lekki, wadanda sai an tsallake gadoji ake zuwa gare su. Hakan na nufin wanda ya bi ta mota ka iya haduwa da cunkosan motoci a kan hanya.
Irin cunkoson da ake haduwa da shi a hanyoyin mota
Hanyoyi marasa kyau da ambaliyar ruwa a damina da kuma jerin kananan motocin da ke kan hanyoyi sune ke kara ta'azzara matsalar sufuri a Lagos. Ana sa ran sabbin tashoshin jiragen kasa da aka bude su rage karfin cunkoson da ake fuskanta.
Samar da hanyar sufuri mai alkinta muhalli
Amma ba da jimawa ba ana sa ran jama'a da dama su rungumi hawa jirgin ruwa saboda gagarumin shirin fadada sufurin jirgin ruwa. Shirin ‘Omi Eko’ da gwamnatin Faransa karkashin hukumar Agence Française de Développement da kungiyar tarayyar suka dauki nauyinsa na da niyyar samar da jiragen ruwa na zamani da zummar rage cunkosan ababen hawa da ke fitar da sinadarin carbon dioxide mai gurbata muhalli.
Yadda tashar jirgin ruwa ta Ikorodu ke hade unguwannin Lagos
Gwamnatin Jihar Lagos ta sanar da gagarumin shirin inganta harkar sufuri. Lagos na daya daga cikin biranen duniya masu cunkosan jama'a da ke bunkasa cikin hanzari. Hukumar AFD ta Faransa ta ce sufuri ta teku shi ne maslaha ga cunkoson da ake yawan samu a titunan Lagos.
Lokaci mai cike da kalubale
A nan fasinjoji na zaman jiran zuwan jirgin ruwa na gaba da za su hau. Da yawan mutane, rayuwar Lagos cike take da kalubale a tsaka da tsadar rayuwar da ta addabi kasar, inda ake yawan samun karin farashin abinci da man fetur da ke samar da hauhawar farashin kayayyaki.
Tabbatar da tsaron lafiyar fasinja
Cunkoson ababen hawa da abubuwan da yake haddasawa sune manyan kalubalen mazauna Lagos, amma sun riga sun saba. Wasu na rage tuka motoci ko kuma hawa motocin haya. Amma idan har za su hau jirgin ruwa to sai sun sanya rigar ruwa domin samar musu da tsaro ko da wani abu zai faru a cikin teku.
Maslaha ta mai tabbas daga hanyoyin da ke da cunkoso
Ruwan da ya raba Lagos gida biyu, ya sanya wajibi a dauki hawa jirgin ruwa a matsayin maslaha. ''Muna kallon sufurin jirgin ruwa a matsayin hanyar da za ta kawo mana dauki daga cunkosan titunanmu.'' in ji shugaban hukumar sufurin jiragen ruwa ta Jihar Lagos Oluwadamilola Emmanuel.
Za a kara yawan jiragen da ke jigilar fasinja a cikin teku
A cikin shekaru uku masu zuwa, ana sa ran bude hanyoyin sufurin ruwan guda 15 tare da samar da jirage masu amfani da lantarki 75. Domin ka da a kara dora wa rumbun adana lantarkin Lagos da ba ya wadatar da jama'an gari, za a samar da injuna masu amfani da hasken rana da jiragen za su rika amfani da su.