Kafa SWAT na fuskantar suka a Najeriya
October 14, 2020Cikin wata sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan ta Najeriyar Frank Mba ya sanyawa hannu, ta bayyana cewa kafa wannan sabuwar runduna ta musamman da ke da dabarun yaki da muggan laifuka da sarrafa makamai da aka lakabawa suna SWAT, wacce kuma ta maye gurbin tsohuwar rundunar musamman mai yaki da 'yan fashi da makami ta SARS da zanga-zanga da matsim lamba ya sanya rusata, a yanayin na ba da kai bori ya hau da gwamnatin ta yi.
Karin Bayani: Najeriya: Murna bayan rusa rundunar SARS
To sai dai ga Deji Adayanju shugaban kungiyar Concerns Nigerians da ke ci gaba da zanga-zanga, su kam ba su yarda da wannan sabuwar runduna da SWAT ba.
Rundunar 'yan sandan Najeriyar dai, ta zayyana sharuddan rundunar farawa daga Larabar wannan makon, matakan da suka hada da bincike a kan yanayin hankali da kamalar kowanne dan sandan da zai kasance cikin rundunar da kuma lafiyarsa, tare da fara horas da su domin samun kwarewa.
A yayin da masu zanga-zangar suka ci gaba da kawo cikas a birnin Abuja, inda suka yi cincirundo a unguwar Berger da ke birnin, kungiyar matasan arewacin Najeriyar ta bayyana ra'ayinta tare da kashedin fara tata zanga-zangar a daukacin yankin arewacin kasar.
Karin Bayani: Fargaba kan zanga-zangar da ke wakana a Najeriya
A cewar dakta Suleiman Shuaibu Shinkafi mai sharhi a kan al'amurran yau da kullum a Najeriyar, ya kamata a yi taka tsan-tsan. Gwamnatin Najeriyar dai na kara bayar da tabbacin gudanar da garambawul a harkar 'yan sandan kasar. Abin jira a ganin shi ne yadda za ta kaya a tsakanin gwamnatin Najeriyar da kungiyoyin da ke ja-in-ja a kan wannan al'amari da ke kara daukar hankali a ciki da wajen kasar.