1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta ci kamfaniin Meta tarar miliyoyin dala

Abdoulaye Mamane Amadou
July 20, 2024

Hukumomi a Najeriya sun sanar da cin kamfanin Meta mamallakin Facebook da WhatsApp tarar dala miliyan 220 bisa zarginsa da taka dokokin kare bayanan masu amfani da shafukan bila-adadin.

https://p.dw.com/p/4iXlk
Hoto: Dado Ruvic/Illustration/File Photo/REUTERS

Hukumar da ke sa ido kan kare hakkin masu amfani da Intanet FCCPC ta bayyana kamfanin Meta a matsayin wanda ya shafe lokaci yana taka dokokin Najeriya.

Karin bayani : Cin zarafi ta kafofin sadarwa na sada zumunta

Hukumar ta ce a iya binciken da ta gudanar daga watan Mayun 2021 zuwa Disamban 2023, ta gano cewa kamfanin Meta ya yi amfani da bayanan dumbin 'yan Najeriya masu amfani da shafukansa ba tare da saninsu ba, sannan an tauye musu 'yancin samun karin haske a kan yadda aka yi amfani da muhimman bayanansu na shafukan.

Karin bayani : Najeriya: Takaddamar gwamnati da Twitter

Kakakin kamfanin WhatsApp guda daga cikin rukunan kamfanin na Meta ya bayyana cewa suna sane da hukuncin, kuma za su daukaka kara.