Najeriya ta fasalta dokar hako man fetur
July 15, 2021Talla
A wannan Alhamis, majalisar dattijan Najeriya ta kada kuri'a amincewa da dokar sake fasalta harkokin man fetur din kasar, mataki da ke zama na karshe da suka yi aiki a kai a 'yan kwanakin bayan nan, bayan shafe shekaru da dama da kudirin ke a gabansu.
Guda daga cikin abin da sabuwar dokar za ta kunsa shi ne bai wa kaso 3 cikin dari na adadin kudaden shiga da kasar ta samu daga albarkatun mai zuwa ga yankunan da ake hakar man.
Majalisar wakilai za ta yi nata zama a kan wannan kudirin dokar kafin daga bisani a tura wa shugaban kasa Muhammadui Buhari da zai sa mata hannu ta zama doka.