Najeriya da Birtaniya za su bunkasa kasuwanci
August 29, 2018A lokacin ganawar tasu Shugaba Buhari da Firamnista May wacce ta isa a Najeriyar tare da tawagar wasu manyan 'yan kasuwa na kasar ta Birtaniya, sun rattaba hannu kan wasu jerin yarjeniyoyi guda biyu da suka shafi tsaro da batu na inganta tattalin arziki. Ko baya ga Abuja May za ta kuma kai ziyara a birnin Lagos cibiyar kasuwancin Najeriyar.
Dama dai makasudin wannan ziyara ta Firaministar May shi ne aza harsashin sabuwar dangantaka da takwarorinsu na Afirka da nufin magance gibin tattalin arziki da kasarta za ta iya fuskanta idan ta raba gari kwata-kwata da Kungiyar Tarayyar Turai. Cikin jawabin da ta yi a jiya Talata bayan isarta birnin Cap na Afirka ta Kudu da ke zama tsani na farko na wannan ziyarar da ta soma, May ta sanar da burinta na sanya Birtaniya a sahun farko na kasa mai karfin arziki da ke huldar kasawanci da Afirka kan nan da shekara ta 2022.
Tun bayan kuri'ar raba gardama ta ficewa daga EU ta watan Maris na 2016, London ta matsa kaimi a fannin diplomasiyya don samun karin yarjejeniyoyin kasuwanci da za su maye gurbin wadanda take da su da Kungiyar Tarayyar Turai. Theresa May ta bayyana matakin zuba jari na Dala miliyan dubu hudu a kasashen Afirka . Ita dai Ingila ta kasance a matsayi, na biyu, na kasashen da suka fi zuba jari a Afirka baya ga Amirka.
Baya ga Afirka ta Kudu da Najeriya, Firaministar Birtaniya za ta wuce Kenya Ranar Alhamis.