1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta manta da 'yan Damasak sama da 400

Uwais Abubakar Idiris/USUMarch 29, 2016

Kungiyar kare hakin jama’a ta Human Rights Watch ta nuna damuwa na rashin jin duriyar yara 'yan makaranta da mata kimanin 400 da aka sace a garin Damasak shekara guda.

https://p.dw.com/p/1ILX9
Symbolbild Entführungen von Frauen und Mädchen in Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/D. Kurokawa

To batun sacewa ko garkuwa da jama’a musamman mata da ‘yan makaranta a daukacin yankin arewa maso gabashin Najeriya dai ya kasance abinda aka dade ana fama da shi, to sai dai matan da ‘yan makanranta na garin Damasack da aka sace shekara guda kenan, sun dauki hankalin kungiyar kare hakkin jama’a ta Amnesty International ne saboda abin da ta kira rashin nuna damuwa da ma kulawa daga bangaren gwamnatin Najeriyar da sauran kungiyoyi, wadanda sai batun 'yan matan Chibok kawai ake ji suna yi.

Domin kuwa adadin yaran da matan da suka haura 400 na nuna adadi mafi yawa da ake da masaniyar sace su a matsalar ta’adanci da ke faruwa a yankin, musamman in an kwatanta da ‘yan matan Chibok da a kullum ake gangami a kansu, amma kuma duk da haka kusan an shiga yanayi na mancewa da lamarin, in banda iyayen yaran da a kullum ke cikin radadin mummunan abin da ya faru da yaransu. Mausi Segun ita ce jami’ar kungiyar Human Rights Watch da ta gudanar da wannan bincike na sake dago batun ta bayyana abin da suke tsoro.

A watan Disambar 2014 ne dai yayan Boko Haram suka kai hari a garin Damasak inda suka afkawa makarantar firamare ta Zanna Mobarti, inda aka yi wannan aika-aika. Shekara guda cikin wannan hali na rashin sanin inda yayan nasu suke ya jefa iyayen yara na Damasak cikin mawuyacin hali, musamman rashim ambato duk wani kokari da ake yi. Wasu daga cikinsu sun bayyana mana rashin jin dadi.

Nigeria Armee rettet Mädchen Symbolbild
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Ikechukwu

Sanin cewa sojojin Najeriya suna ci gaba da samun nasarar kwato mutanen da aka sace ko garkuwa da su, ko me yasa har yanzu babu wani labari a game da yaran na Damasak daga bangaren sojojin da ma gwamnatin Najeriya? Kanar Sani Usman Kuka Sheka shi ne kakakin rundunar sojan Najeriya, wanda ya nuna cewa suna kokari kwato wadanda aka sace.


Ga kungiyar ta Human Rights Watch dai na mai kira ga gwamnatin Najeriyar ta dauki mataki cikin gaggawa kamar yadda Mausi Segun ta bayyana wa DW.

Abin jira a gani shi ne ko dago batun da Human Rights Watch ta yi zai yi tasiri musamman wajen sake zaburara da laluben daukacin mutanen da aka sace da ma bude rijista abin da zai taimaka sosai bisa tsarin da ake amfani da shi na kasa da kasa a kan irin wannan matsala.