Najeriya ta rage farashin fetur ga 'yan kasar
March 18, 2020Wannan na nufin ke nan kasar ta rage akalla Naira 20 a kan farashin litar man fetur. Gwamnatin kuma ta ce sabon ragin zai fara aiki ne nan take.
Karamin Ministan Man fetur Timpre Sylva ne ya sanar da wannan mataki a ranar Laraba kamar yadda wakilinmu na Abuja Ubale Musa ya ruwaito mana.
Tun a shekara ta 2016 ne dai gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kara kudin man fetur daga Naira 87 da ta iske a hannun gwamnatin Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ta kuma mayar da shi zuwa Naira 145 a kan kowace lita, lamarin da ya haddasa cece-kuce a kasar. Ana dai ganin ragin farashin na ranar Laraba ya faru ne a sakamakon yadda darajar fetur din ta fadi a kasuwar duniya.
Sai dai kuma hukumomi sun ce farashin ka iya sauyawa idan darajar fetur din ta kara dagawa ko kuma ta sauka a kasuwannin duniya.