1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fitar da albarkatun man fetir a Najeriya na ganin tasku

Yusuf BalaMay 10, 2016

Tuni dai wasu kamfanoni suka fara janye ma'aikatansu daga wurin da ake hakar albarkatun na man fetir a yankin Niger Delta.

https://p.dw.com/p/1Il58
Elektrizität Afrika
Wurin aikin albarkatun man fetir a birnin Port HarcourtHoto: Getty Images/AFP/F. Plaucheur

Abin da Najeriya ke fitarwa a harkar hakar manfetir ya samu koma baya da ke zama mafi muni cikin shekaru 22 da suka gabata kamar yadda kididdiga ta nunar a ranar Talatan nan. Abin da ke zuwa bayan da 'yan waye da ke dauke da makamai suka koma aikinsu na fasa butun mai a yankin Niger Delta. Wannan dai ya sanya da dama cikin kamfanoni da ke hakar albarkatun a wannan yanki suka kwashe ma'aikatansu.

A cewar kamfanin Bloomberg da ke a birnin New York wanda ke bibiyar kai kawo na hada-hadar irin wadannan albarkatu, ya ce kasar ta Najeriya wacce ke kan gaba wajen fitar da albarkatun man fetir a Afirka ta samu koma bayan samun kasa da ganga miliyan daya da dubu dari bakawai a rana abin da ke zama karon farko tun daga shekarar 1994.

'Yan tawayen dai na Niger Delta na kara zama wata barazana ga kasar ta Najeriya ganin yadda suka tasamma karasa gurguta abin da kasar ke alfahari da shi wajen samun kudin shiga wanda tuni farashinsa ke ji a jika a kasuwar man fetir ta duniya.