Najeriya ta sanar da kudin Hajjin 2025
January 20, 2025Hukumar kula da aikin hajjin ta Najeriya watau NAHCON ta nuna cewa kudin aikin hajjin zai fara ne daga Naira milyan takwas da dubu dari bakwai ga maniyata daga yankin kudancin Najeriyar yayinda maniyata daga yankin jihohin Adamawa da Borno zasu biya Naira milyan takwas da dubu dari uku su kuma maniyata daga sauran yankin arewacin Najeriyar zasu biya Naira milyan takwas da dubu dari hudu. Wannan ya nuna cewa wasu shiyoyin kasar sun biya kasa da wannan farashi, to sai dai wadanda suka biya kujerun ba tare da tallafin da gwamnati ta bayar ba, domin sun biya kusan milyan 10 a bara. Sanin cewa a wannan shekarar duk da janye tallafi aikin hajji da koma bayan tattalin arziki wace dabara suka bi suka cimma wannan? Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan shine shugaban hukumar aikin hajji ta Najeriyar. Yace hukumar alhazan ta sanya wa'adi zuwa karshen watan Janairu ga duk mai niyyar zuwa aikin hajji ya kamala ya biya kudin domin wa'dain da kasar Saudiyya ta bayar kenan.
Kodayake hukumar na kalon an samu sauki na barin kudin aikin hajjin na bana a zagayen yadda yake ga wasu sassan yayinda aka samu kari ga maniyatta daga kudancin kasar amma janyae tallafi ya sauya al'amarin. Alal misali a 2024 wadanda suka samu amfana da tallafin Naira bilyan 90 da gwamnatin ta bayar sun biya Naira milyan shida da dubu dari takwas daga dukkanin sassan Najeriyar, yayinda maniyata daga yankin kudancin Najeriyar da basu amfana da tallafin ba suka biya Naira milyan takwas da dubu dari hudu maimakon milyan takwas da dubu dari bakwai da za su biya a 2025. Alhaji Kabiru Abubakar na cikin maniyata aikin hajjin bana ya bayyana yadda yake kalon kudin aikin hajji na bana.
Tuni dai hukumar alhazan ta Najeriya ta fitar da sunayen kamfanonin jiragen saman da za su yi jigilar mahajattan na Najeriya a bana wadanda suka hada da na cikin kasar da na kasar Saudiyya. Ana nuna damuwa a kan daya daga cikin kamfanonin Max Air saboda gaza biyan bukatar masu harka da su a Najeriya. Prince Anofiu Olarewanju shine kwamishinan gudanarwa na hukumar alhazan Najeriyar.
‘'Yace tsari ne mai kyau muka bi wajen zaben kamfanonin jiragen mun yi la'kari da kwarewa Mun kuma duba lafiyara jiragen da suke wo haya domin wannan aiki, fatanmu mu inganta aka aikin hajjin da muka yi a bara''
Maniyatan hukumar aikin hajjin ba za ta maimaita abinda ya faru a bara ba inda daga baya ta sake fito da kudin aikin hajji saboda tsadar dallar Amurka da ya shafi shirin da maniyata da dama suka yi.
Fitar da kudin aikin hajjin da amincewa da kamfanonin jiragen sama da za su yi jigilar mahajattan ya nuna fara shirye-shiyen aikin hajjin adadin maniyata dubu 95 da aka bata a wannan shekarar wadanda har yanzu suke fatan gwamnati ta sake maido da tallafin aikin hajji ta yadda za su samu sauki.