1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Najeriya ta shirya yaki da barayin daji

January 6, 2022

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya tabbatar da ayyana 'yan fashin daji da ke addabar mazauna arewaci da ma wasu yankuna na kasar a matsayin cikakkun 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/45DWX
Muhammadu Buhari, Präsident von Nigeria
Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya yi bayanai kan batutwa da suka shafi Najeriya a wata hira da tashar talabijin ta Channels da ke kasar, ya ce ya kitse zancen da jagororin tsaro kuma tuni gwamnati ta fara murkushe 'yan bindigar.

Daga yanzu a cewar Shugaba Buhari, matsayin duk wasu da ke rike da makamai 'yan ta'adda ne kawai, za kuma a tinkare su da dukkanin karfi da zai dace da su.

Najeriyar wacce ke fama da dumbin matsaloli musamman na tsaro, ta cefano wasu jiragen yaki daga Amirka wadanda bisa doka sai manyan takadarai ne za a tinkara da su.

Shugaba Buhari dai na shan suka daga bangarori da dama na kasar saboda jinkirin daukar matakai a kan 'yan bindigar da ke kashe-kashen jama'a, kashe-kashen kuwa da ya yi alkawarin kawo karshen su a lokacin yake yakin neman zabe.