1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta ware makudan kudi don yakar Ebola

August 8, 2014

Shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan ya ce gwamnatinsa ta ware dalar Amirka miliyan sha daya da rabi domin tunkarar cutar nan ta Ebola wadda ta bulla a kasar.

https://p.dw.com/p/1CreM
Spanien Madird Überführung Ebola Miguel Pajares Patient
Hoto: Reuters

Shugaban ya bayyana hakan ne a wannan Juma'ar, inda a hannu guda bayan kammala wani taro na gaggawa da ya kira ya ce kasar ta bi sahun hukumar lafiya ta duniya wajen ayyana dokar ta baci kan cutar ta Ebola a Najeriya.

Tarayyar ta Najeriya da ke da kan gaba wajen yawan al'umma a Nahiyar Afirka ta bayyana bullar cutar ce a tun bayan da aka gano wani dan kasar Liberiya da ya shiga kasar wanda ke dauke da cutar wadda ta yi ajalinsa da kuma wata ma'aikaciyar jinya da ta kula da shi.

Ya zuwa yanzu dai hukumomin lafiya a kasar sun ce wasu karin mutane sun nuna alamu na kamuwa da cutar kuma tuni ma aka killacesu kuma ake cigaba don yi musu magani tare da sanya idanu kan 'yan kasashen waje da ke shige da fice ciki kasar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal