1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta yaba basirar Merkel a taron G20

July 8, 2017

Gwamnatin Najeriya ta yaba tsayuwar Jamus kan fifta Afirka a taron G20 da aka kammala. Mukaddashin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce fifita matsalolin da ke nahiyar Afirka da Merkel ta yi, abin jinjina ne.

https://p.dw.com/p/2gCkl
Deutschland G20 Gipfel Retreat Sitzung
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce tilas ne a jinjina wa shugabar gwamnatin Jamus Angela saboda fifita kokarin ci gaban nahiyar Afirka tad a yi a taron kasashen G20 da aka kammala a nan Jamus.

Gabanin taron kolin birnin na Hamburg dai, sai da aka yi zaman hadin guiwa tsakanin gwamnatocin kasashe masu karfin masana'antun da na Afirka a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus kan yanda za a maganta matsalolin arziki da siyasa da ke a kasashen na Afirka.

Mukaddashin shugaban na Najeriya ya kuma ce lokaci ya yi da za a ga matakan kyautata al'amura a Afirka a zahiri, ba kuma zafin turanci ko alkawura ba, ta la'akari da yarjejeniyoyin da kasashen suka cimma.

A cewar Osinbajo, kasashen Jamus da Faransa da Italiya da ma kasar Birtaniya, kamata ya yi su tabbatar da ganin sun yi mai yiwuwa cikin kwanaki kalilan don ganin jifa ta dace da waiwaye.

Hakan kuwa na zuwa ne a dai dai kuma lokacin da kungiyar tarayyar Turai a nata bangaren ke kokarin kammala tsara wasu matakai kan yaki da sato kudade daga kananan kasashen da ake jibge su a ketare.