Najeriya: Martani kan karin albashi ga ma'aikata
March 30, 2023Labari ne mai dadin ji ga daukacin ma'aikatan gwamnatin Najeriyar da ma kungiyar kwadago ta kasar da ta kasance kan gaba wajen neman a yi wa ma'aikatan karin albashi saboda wahalhalun da suke fuskanta na hauhawan farashin kayayyaki da ba a taba gani ba a kasar. Dama gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti da ya dauki lokaci mai tsawo yana tattaunawa a kan yadda za'a aiwatar da karin albashin da bisa ka'ida ya kamata a yi wa ma'aikata bayan kowane shekaru biyar. Dr Chris Ngige shine minsitan kwadago da igantuwar aiki da ya yi karin haske a kan karin albashin.
Kowane ma'aikacin gwamnati zai samu karin albashi, mun riga mun amince da shi a kwamiti kuma zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairu, An tsara shi ne don rage radadin hauhawan farashin kaya da tsadar rayuwa, karin kudin waya da kudin wuta lantarki. Karin zai fara aiki ne daga 1 ga watan Janairun wannan shekara, an riga an sanya kudin a kasafin kudin wannan shekarar don haka ba bukatar a ce shugaban kasa muna san a duba wannan, akwai kudin an kasafta su''.
Dama kungiyar kwadagon Najeriyar ta dade ta na jira a kan wannan batu bisa alkawarin da gwamnatin tarayya ta yi cewa za ta kara wa ma'aikata albashi kafin watan Mayu da za ta sauka daga mulki. Kungiyar kwadagon ta kai ga barazanar shiga yajin aiki a kan matsalar tsadar rayuwa. Comrade Nasiru Kabiru sakataren tsare-tsare na kungiyar kwadagon Najeriyar ya ce sai sun gani a kasa tukunna.
Sanin cewa ministan bai baiyyana ko kashi nawa ne aka kara na albashin ba, sai dai ya ce dama ba wai sabon albashi suka yi wa ma'aikatan gwamnatin Najeriyar alkawari ba. Ga Comrade Nasiru Kabir ya ce akwai alkawarin da suka cimma da gwamnatin.
Duk da muranar da ake yi na samun karin albashi ga ma'aikatan gwamnatin Najeriya ana tsoron yadda karin albashin ga ma'aikatan da basu wuce milyan daya ba zai haifar da hauhawan farashin kaya a kasar. Dama Najeriyar na cikin matsala ta hauhawan farashi mafi muni a cikin shekaru 17 ga suka gabata. To sai dai ga Mallam Yushau Aliyu masanin tattalin arziki ya ce akwai bukatar fahimtar yadda lamarin yake.
Maikatan gwamnatin Najeriya dai na cikin wadanda ke karbar albashi mafi kankanta a duniya, inda suke karbar Naira 30,000 a wata, albashin da suka koka baya kai su ko ina saboda tsadar farashin kaya. Abin fargaba ne bar wa gwamnati mai jiran gado wannan nauyi na karin albashi da ke cike da sarkakiyar gaske a Najeriyar, domin me ake jira da karin albashin da gwamnati ta ce an sanya shi a kasafin kudi.