1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Babu tushe a gargadin Amirka

Abdoulaye Mamane Amadou ATB
October 31, 2022

Hukumin tsaro a Najeriya sun yi watsi da gargadin kai hare-hare a babban birnin tarayya Abuja da wasu manyan kasashen yammacin duniya suka yi.

https://p.dw.com/p/4ItuI
Der nigerianische Präsident Buhari besucht den Bundesstaat Borno
Hoto: Bayo Omoboriowo

Hukumomin tsaro a tarayyar Najeriya sun yi fatali da barazanar yiwuwar kai harin ta'addanci a babban birnin tarayya Abuja, kwanaki bayan da ofishin jakadancin Amirka ya yi irin wannan gargadi tare da umartar ma'aikatansa su fice daga birnin.

Jim kadan bayan wani taron koli da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranta a wannan Litinin, babban jami'in da ke ba shugaban Najeriyar shawara kan tsaro Babagana Monguno ya ce gargadin da ofishin jakadancin Amirkar ya fitar karya ce tsagwaronta, tare da fatan ganin daukacin al'ummar da ke fargaba sun koma bakin aikinsu ba tare da wani shakku ba, saboda abinda ya kira kokarin da gwamnatin Najeriyar ta ke yi da tallafin abokan huldarta na kasa da kasa don tabbatar da tsaro.

Tuni ma dai aka ruwaito kara karfafa matakan tsaro a babban birnin na Abuja, tun bayan gargadin da ofisoshin jakadancin kasashen Amirka da Canada da Birtaniya suka yi a makon da ya gabata.