Najeriya:Takun saka kan gyaran kundin tsarin mulki
December 20, 2017Kama daga 'yanci na cin gashin kai a mataki na kananan hukumomi a Najeriya ya zuwa tabbatar da 'yan sanda na jihohi da ma uwa uba sa ke tsarin dimokradiya da rabon kudin tsarin mulki ya sa aka dauki lokaci game da bukatar sauyin fasalin lamura a kasar. Sai dai ana shirin fuskantar rikici sakamakon matakin majalisun tarayyar biyu na tsallake gwamnoni na jihohi tare da mika bukatar gyaran ga majalisun jihohi na kasar kai tsaye.
Batun ya harzuka gwamnonin kasar da suke karatun yankan baya a bangaren 'yan dokan da ke neman 'yanci iri-iri amma kuma ke tsoron zartarwa. Kokari na gyara na kasa ko kuma cika burin son ran dai ga 'yan majalisun dokokin na zama babbar dama ta sauyi na rawa a bangaren 'yan dokar da suka dauki lokaci suna ji a jiki a cewar Yusuf Abdullahi Atta shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano a arewacin kasar. Yanzu haka dai an zuba ido wajen ganin tasirin da muhawarar da ke dada kamari cikin kasar mai shirin gudanar da zabe nan ba da jimawa ba.