1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaduna: Takaddama a tsakanin gwamnati da ma'aikata

Ramatu Garba Baba
May 21, 2021

Yajin aikin Kungiyar Kwadagon Najeriya ya fuskanci suka a sassan kasar bayan da kungiyar ta ja daga har zuwa lokacin da aka biya mata bukatunta.

https://p.dw.com/p/3tfpw
Nigeria Abuja | Protest für Mindestlohn vor Nationalversammlung
Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

A Jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya, matakin Kungiyar Kwadago ta (NLC) sun kawo karshen yajin aiki na gargadi a sakamakon korar wasu ma'aikatan da gwamnan jihar Nasir el-Rufai ya yi tare da zabtare musu kudaden albashi, ya soma daukar hankula inda gwamnatin tarayyar Najeriya ta soma nazari kan batun da ya gurgunta duk kai-kawo a jihar Kaduna.

Gwamnan jihar Nasir el-Rufai dai, ya dage kan korar da ya yi wa ma'aikatan amma kuma 'yan kwadagon sun ce dole ne ya ci tuwon fashi. An kwashi fiye da kwanaki uku kafin aka kawo karshen yajin aikin, rahotanni sun ruwaito yadda yajin aikin ya gurgunta al'amura har dama jefa jihar cikin duhu a sakamakon dagewar da gwamnan yayi kan matsayinsa.