Tsada da kuncin rayuwa a Najeriya
July 20, 2022Karo na biyu kenan dai a jere a cikin wannan shekarar, babban bankin Najeriyar na kara kudin ruwa a kan bashin da masana'antun kasar da ma daidaikun mutane ke karba, daga kaso 13 cikin 100 zuwa kaso 14 cikin 100. Wannan dai na nuni da hali na matsi da ma koma bayan da ke fuskantar tattalin arzikin kasar domin farashin kaya na ci gaba da ninkawa, inda ba ka da tabbas a kan nawa zaka sayi kaya bayan yini guda. Gwamnan babban bankin Najeriyar Godwin Emefiele ya ce a nasu hasashen kara kudin ruwan ne mafita wajen shawo kan hauhawar farashin kayan masarufin a kasar. To sai dai a baya babban bankin na Najeriya da aka dorawa alhakin kula da manufofi na tattalin arziki da suka shafi darajar Naira da hauhawan farashin kaya, ya yi irin wannan kari kuma maimakon ragi abin ma karuwa ya yi.
Wannan dai na faruwa ne a daidai lokacin da Najeriyar ta kara farashin kudin man fetir, saboda mayar da NNPC zuwa kamfani mai zaman kansa maimakon na gwamnati. Duk da arzikin man fetur da Najeriyar ke da shi dai, yana daga cikin kayayyakin masarufi da take shigowa da su daga waje. Najeriyar dai na shigo da tattacen man fetur daga ketare ne, abin da ke zama babban kalubale ga kasar musamman saboda yadda yaki tsakanin Rasha da Ukraine ya canza yadda harkoki ke gudana a duniya. Da alamun babban bankin kasar sai ya sake karatun ta natsu, domin ceto kasar da tattalin arzikinta ke fama da masassara.