Najeriya: Yajin aikin likitoci ya dagula harkoki
August 27, 2024Lokitocin dai sun fara yajin aikin domin nuna fushinsu kan wata "yar kungiyarsu da "yan bindiga suka sace a watan Disambar bara, lamarin da wasu mutanen ke cewa yajin aikin bai dace ba, domin talakawa ne wadanda ba su ji ba ba su gani ba ne za su sha wuya.
Kungiyar likitocimasu neman kwarewa ne dai suka shiga wannan yajin aiki domin nuna rashin jin dadin su dangane da kama yar uwar su da masu garkuwa suka yi,kuma har yanzu hukumomi ba su iya kubutar da ita ba. Lamarin da ya jawo tsayawar lamura a manyan asibitocin da ke fadin Nigeria. Salamnu Bala da muka iske ya kai marar lafiya asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano yace yanzu ba su san in da za su saka kansu ba kasancewar sun dauko marar lafiyar ne tun daga Jihar Adamawa gashi ba su san in za su dosa ba.
Dr.muhammad Dawaki shi ne shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa reshen Kano, ya ce kamun da aka yi wa ma aikaciyar ta su cin fuska ne shi ya sa dole suka fara yajin aikin gargadi. To amma masana da masu fashin baki na sukar lamirin likitocin bisa jefar rayuwar mutane cikin garari alhalin ba su ji a ba su gani ba. Abubakar Ibrahim masharhanci ne kan lamuran yau da kullum ya ce wannan yjin aiki tamkar an bar jaki ne ana dukan taiki. Yanzu haka dai marasa lafiya da dama ne ke fuskantar matsala in da suke shiga asibiti daga wasu jihohin kuma babu batun ba su kulawa.