1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yajin aikin NLC bai samu karbuwa ba

Ubale Musa daga AbujaMay 18, 2016

'Yan kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC sun gudanar da zanga-zanga a Abuja da ma shiga yajin aiki kan karin kudin mai duk kuwa da hani da kotu ta yi musu na yi haka.

https://p.dw.com/p/1Iq0A
Nigeria Arbeiterkongress protestiert 2010
Hoto: dapd

NLC dai ta ce ta kaddamar da yajin aikin sai baba ta gani da nufin tilasta gwamnatin kasar dawowa daga dokin karin wanda shi ne irinsa na farko da gwamnatin Shugaba Buhari ya yi. 'Yan kwadagon dai sun ce ba wata hujja ta yin karin kudin mai, wannan ne ma ya sanya shugaban kungiyar Ayuba Wabba ya ce suka ga dacewar shiga yajin aikin.

To sai dai daga dukkan alamu yajin aikin ya raba kan su kansu yan kwadagon kasar inda takwarar kungiyar NLC wato TUC ta ce ba ruwanta da shiga wannan yajin aiki. Comrade Bobboye Bala Kaigama da ke zaman shugaban kungiyar ta TUC ya ce sun janye ne saboda tabbaci da suka samu daga hukumomi cewar janye tallafin man da karin farashinsa zai kai ga daidaita lamura a kasar.

Tuni dai gwamnatin Najeriya din ta ce ta na kallon wannan yajin aiki da 'yan kungiyar ta NLC suka kira da idon basira kuma za ta dauki mataki in hali ya yi kamar yadda ministan sharir kasar Abubakar Malami ya shaidawa wakilin DW a Abuja a wata hira da suka yi da shi. Bisa ga binciken da wakilinmu ya gudanar dai yajin aikin bai samu karbuwa ba a wurare da dama ciki kuwa har da babbar sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Yanzu haka dai 'yan Najeriya na cigaba da zuba idanu don ganin wannan dambarwa tsakanin gwamnati da 'yan kwadagon za ta kaya da kuma yadda su kansu 'yan kwadagon za su shawo kan ma'aikata domin su shiga yajin aikin gada-gadan kamar yadda suke so don yin matsin lamba ga gwamnati ta maida kudin man fetur din kamar yadda ya ke a baya.

1. Mai in Nigeria
Maimakon shiga yajin aiki, wasu 'yan Najeriya sun yi zanga-zanga ta goyon bayan cire tallafin maiHoto: DW
Nigeria Tankstelle in Lagos
'Yan kwadago na son a janye karin kudin mai da gwamnati ta yiHoto: AFP/Getty Images/P. U. Ekpei