'Yan bindiga sun kai wa 'yan sandan Najeriya hari
April 20, 2021Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra Nwode Nkeiruka ya sa wa hannu, ya ce mayakan da ke dauke da makamai sun mamaye hedikwatar ‘yan sanda da ke Upko, a jihar Anambra, da kuma wani ofishin‘ yan sanda a makwabciyar jiha ta Abia. Sai dai an bayyana cewar ‘yan sanda biyu sun samu raunika, yayin da mahari daya ya riga mu gidan gaskiya lokacin da suka yi musayar wuta tsakaninsu.
Babu wata kungiya da ta dauki alhakkin kai hare-haren ya zuwa yanzu. Amma yankin kudu maso gabashin Najeriya ya fara kaurin suna a fuskar kai hare-hare a kan jami’an tsaro, wanda hukumomi ke dangantawa da kungiyar aware ta Ipob da ke fafutukar neman‘ yancin Biafra.
Makonni biyu da suka gabata ma dai, wani mummunan harin da aka kai a gidan yari a Owerri, babban birnin jihar Imo, ya bai wa fursunoni sama da 1,800 damar tserewa. Sai dai Kungiyar Ipob ta musanta cewa tana da hannu a wannan tserewar fursunoni mafi girma a tarihin Najeriya.