1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaduna: An yi garkuwa da wasu Kristoci

Ramatu Garba Baba
May 9, 2023

Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 20 daga wani coci da ke kauyen Madallah na karamar hukumar Chikun a jihar Kadunan Najeriya.

https://p.dw.com/p/4R4YP
Hoton makarantar Bethel da aka yi garkuwa da dalibai a shekarar 2021
Hoton makarantar Bethel da aka yi garkuwa da dalibai a shekarar 2021Hoto: AFP via Getty Images

Mutum akalla arba'in wasu da ake zargin 'yan bindiga ne, suka yi garkuwa da su a jihar Kaduna da ke arewacin kasar. Maharan sun afka kan masu ibada a cocin Bege Baptist da safiyar ranar Lahadin da ta gabata in da suka yi garkuwa da kusan duk mutanen da suka riske a cocin. Shugaban Kungiyar Cocin Katolika reshen jihar Kaduna Ravaran Joseph Hayaf ya tabbatar da labarin yana mai cewa da farko mutum arba'in aka tafi da su amma daga bisani, sha biyar daga cikinsu sun yi nasarar kubuta daga hannun 'yan bindigan.

Wannan na zuwa ne, bayan wani rahoto daga Kadunan da ke cewa, 'yan bindiga sun sace 'ya'yan sarkin Kagarko Alhaji Sa'ad Abubakar da ma wasu jikokinsa da kuma wasu mazauna garin da ke kudancin jihar. Jihar Kaduna na daga cikin jihohin a arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro musanman na masu satar mutane don neman kudin fansa.