Kasashen Turai sun nemi daukar mataki kan 'yan gudun hijira
September 5, 2018Talla
Mutum fiye da dubu dari takwas ne ke cikin tsananin bukatar abinci bayan da aka yanke hanyar isar da tallafin da ake basu, kamar yadda ya ke kunshe a wasikar da kasashen suka aikawa majalisar.
Kasashen da suka kunshi Britaniya da Faransa da kuma Jamus dama kungiyar tarrayar Turai, sun nuna damuwa inda suka nemi majalisar da ta matsa kaimi don ganin gwamnatin Najeriya ta bayar da izinin isar da agaji ga 'yan gudun hijirar da ke a yankin da ya sha fama da rikicin mayakan kungiyar Boko Haram.
Wannan dai na a sabanin ikirarin da gwamnatin Najeriya ke yi, na cewa lamura sun koma yadda suke kuma jama'a sun fita daga cikin kangin da suka tsinci kansu a sanadiyar tashe-tashen hankula da suka biyo bayan ayyukan kungiyar masu tayar da kayar baya.