1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: 'Yan matan Chibok 100 sun rasu

Uwais Abubakar Idris LMJ
April 16, 2018

A Najeriya fitaccen dan jaridar nan da ke kusa da kungiyar Boko Haram, Ahmed Salkida ya ce, 'yan matan sakandaren garin Chibok guda 100 daga cikin 113 da har yanzu suke a hannun kungiyar sun mutum.

https://p.dw.com/p/2w85W
'Yan mata 'yan makarantar sakandaren garin Chibok da Boko Haram ta sace
'Yan mata 'yan makarantar sakandaren garin Chibok da Boko Haram ta saceHoto: youtube/Fgghhfc Ffhjjj

Fitaccen dan jaridar Ahmed Salkida, ya ce 'yan matan sun rasa rayukansu ne sakamakon musayar wuta tsakanin sojojin Najeriya da na kungiyar ta Boko Haram. Wannan batun dai ya janyo mai da martani musamman daga iyaye da ma kungiyar da ke fafutukar ganin an sako su ta Bring Back Our Girls. Wannan dai shine bayani na baya-baya nan game da kokari na sanin hali da ma makomar wadanan 'yan mata na makarantar sakanadaren Chibok da ke jihar Borno, wadan da shekaru hudu kenan cif da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka yi awon gaba da su daga makaranta.

Bayanin da Ahmed Salkida dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnatin Najeriyar ke cewa tana ci gaba da tattaunawa da wadanda ke rike da su, domin ganin an sako su. Kokari na gasgata bayanin nasa yafi rinjaya daga iyayen yaran da kuma 'yan kungiyar ta Bring Back Our Girls fiye da watsi da shi, saboda sanin kusancinsa da kungiyar da ta kai shi ga shiga fushin gwamnatin Najeriyar.

Kungiyar Bring Back Our Girls da ke fafutukar ganin an sako 'yan matan Chibok
Kungiyar Bring Back Our Girls da ke fafutukar ganin an sako 'yan matan ChibokHoto: Reuters/A. Akinleye

Kai ruwa rana a batun ceto 'yan matan

Tun ana wa juna kalon hadarin kaji, ta kai ga tsintarsu a rana a tsakanin 'yan kungiyar Bring Back Our Girls da ke matsin lamba ga gwamnatin lallai ta karbo 'yan matan, musamman bayan abin da ya faru na sace 'yan matan Dapchi da yadda aka samu nasarar karbo su ta hanyar tattaunawa da gwamnati. Nauyin wannan bayani na dan jarida Salkida da a baya gwamnatin ta sanya shi  zama mai shiga tsakanin da kungiyar, ya sanya tuni gwamnatin Najeriyar mayar da martani, inda kakakin shugaban Najeriya Mallam Garba Shehu y ace gwamnati bata da masaniya da wannan bayani da Salkida ya bankado.

Wannan bayani da Salkida ya yi ya kara rura wutar matsin lamba daga iyayen 'yan matan da ma masu fafutuka a kan wannan lamari na 'yan matan na Chibok da ke zama karfen kafa ga gwamnatin. Sai dai a zahiri kai wa ga samun nasarar karbo 'yan matan 107 Na zama abin da mahukuntan ke dogaro da shi ga daukacin lamarin da ke da sarkakiyar gaske. Abin jira a gani dai shi ne abin da zai biyo bayan kalaman na Salkida.